Kasar Amurka Ta Ji Wuta, Za Ta Yi Abin Alheri ga Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
- Gwamnatin kasar Amurka na duba yiwuwar sassauta takunkumin da ta kakaba kan man Iran yayin da farashin mai ke kara tashi a duniya
- Farashin mai da gas na ci gaba da tashi sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke kara zama barazana ga tattalin arzikin duniya
- Gwamnatin Trump na kokarin rage hauhawar farashin makamashi ta kowace hanya domin rage radadin wahalar da aka shiga saboda yakin Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington, US– Gwamnatin Amurka ta fara damuwa da tashin farashin fetur sakamakon yakin da take da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya jawo karancin mai a kasuwannin duniya.
Ministan da ke kula da harkokin baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa gwamnatin kasar na iya sassauta takunkumi kan man Iran da tuni yake kan hanyar jigila domin rage hauhawar farashin makamashi.

Kara karanta wannan
China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Fox News, yayin da farashin mai da gas ke ci gaba da tashi sakamakon rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.
Tasirin yakin Iran a harkokin makamashi
Farashin makamashi ya kara tashin gwauron zabo ne bayan Iran ta kai hari kan babbar cibiyar gas (LNG) a kasar Qatar, tare da yin barazanar lalata sauran cibiyoyin makamashi a yankin.
Bessent ya kuma ce gwamnatin Amurka na duba yiwuwar fitar da karin mai daga rumbunan ajiyar man fetur na gaggawa domin rage radadin matsalar.
Gwamnatin Shugaba Donald Trump na kokarin shawo kan matsalar hauhawar farashin makamashi tun bayan harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Rikicin ya kawo cikas ga sufurin mai
Martanin da Tehran ta mayar ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wanda hakan ya dagula hanyoyin samar da makamashi a duniya.
Kusan kashi daya cikin biyar na danyen mai da gas a duniya na wucewa ta wannan mashigi a lokacin zaman lafiya,cewar rahoton Vanguard.
A halin yanzu, farashin danyen mai na duniya (Brent) ya tashi da kusan kashi 10 kafin ya dan sauka zuwa karin kashi 5, inda ya kai dala 112.76 kan kowace ganga.

Source: Getty Images
Wasu matakan da Amurka ta dauka
A baya-bayan nan, Amurka ta ba da damar sayar da man Rasha da aka sanya wa takunkumi wanda ke kan teku.
Haka kuma, a ranar Laraba, Shugaba Trump ya dakatar da wata tsohuwar dokar jigilar ruwa na tsawon lokaci domin taimakawa wajen rage farashin makamashi.
Amurka ta gano batun nukiliyar Iran
A wani labarin, kun ji cewa hukumar leƙen asirin Amurka ta ce Iran ba ta sake gina cibiyoyin shirin nukiliyarta ba kamar yadda Shugaba Donald Trump ya yi ikirari.
Bincike ya nuna cewa tun da aka lalata cibiyoyin shirin nukiliyar Iran a harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a watan Yunin 2025, har yau ba ta sake ginawa ba.
Daraktar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Amurka, Tulsi Gabbard, ce ta bayyana hakan a rubutacciyar shaida ga kwamitin majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng
