Hukumar Leken Asirin Amurka Ta Gano Gaskiya, Ta 'Kunyata' Trump kan Shirin Nukiliyar Iran

Hukumar Leken Asirin Amurka Ta Gano Gaskiya, Ta 'Kunyata' Trump kan Shirin Nukiliyar Iran

  • Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce Iran ba ta sake gina cibiyoyin shirin nukiliyarta ba kamar yadda Shugaba Donald Trump ya yi ikirari
  • Wannan ya saba da hujjar da Trump ya bayar na kai hare-hare cikin Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025, lamarin da ya jawo barkewar yaki
  • Tulsi Gabbard ta ce an lalata shirin nukiliyar Iran gaba ɗaya tun a yakin farko da aka yi, wanda ya shafe kwanaki 12

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington, USA – Hukumar leƙen asirin Amurka ta bayyana cewa har yanzu kasar Iran ba ta sake gina cibiyoyin sarrafa sinadarin uranium na shirin nukiliya ba kamar yadda ake zargi.

Bincike da hukumar leken asirin Amurka ta yi, ya nuna cewa tun da aka lalata cibiyoyin shirin nukiliyar Iran a harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a watan Yunin 2025, har yau ba ta sake ginawa baN.

Kara karanta wannan

China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: @Anadolu
Source: Getty Images

Rahoton Amurka ya karyata Trump

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan rahoto ya sabawa hujjojin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dogara wajen ci gaba da yaƙi, inda ya yi ikirarin cewa Iran na dab da kera makamin nukiliya.

Daraktar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Amurka, Tulsi Gabbard, ce ta bayyana hakan a rubutacciyar shaida ga kwamitin majalisar dattawa.

Shin Iran na shirin kera nukiliya?

Ta sanar da majalisar cewa harin da aka kai wanda aka kira “Operation Midnight Hammer” ya lalata shirin nukiliyar Iran gaba ɗaya.

“Bayan wannan hari, shirin sarrafa uranium na Iran ya rushe gaba ɗaya, kuma babu wata alama da ke nuna cewa an fara ƙoƙarin sake gina shi," in ji ta.

Sai dai lokacin da take magana kai tsaye a gaban sanatoci, ba ta maimaita wannan bayani ba, lamarin da ya jawo tambayoyi daga ‘yan majalisar.

Kalaman da aka saba ji daga Trump

Kara karanta wannan

Trump ya soki NATO, ya yi magana game da ƙasashen da suka ki taya su yaƙar Iran

Trump ya sha nanata cewa ya bayar da umarnin kai harin kan Iran tare hadin gwiwar Isra’ila ne a ranar 28 ga Fabrairu saboda abin da ya kira, “barazanar gaggawa ga tsaron Amurka.”

Bayan harin na 2025, ya ce Amurka ta lalata cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya, amma daga baya ya sake cewa Tehran na dab da kera bam din nukiliya, duk da cewa masu lura da al’amura da dama ba su yarda da wannan ra’ayi ba.

Jagoran Iran.
Jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A jawabinta ga sanatoci, Gabbard ta ce Iran ta fuskanci manyan hare-hare a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan tsohon jagoran Ayatollah Ali Khamenei.

Sai dai ta ce duk da haka, tsarin gwamnatin Iran har yanzu yana nan daram, duk da yake ya samu rauni sosai, kamar yadda France 24 ta ruwaito.

Trump ya soki harin Isra'ila kan Iran

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald J Trump ya yi gargadi kan rikicin Gabas ta Tsakiya bayan wani harin Isra'ila da filin gas da ke Iran

Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta kai hari kan wani muhimmin wurin hakar gas da ake kira South Pars Gas Field da ke cikin Iran, sakamakon 'fushin' abubuwan da ke faruwa a yankin.

A cewarsa, Amurka ba ta da masaniya kan wannan hari, kuma ba ta da hannu a ko kadan a cikin shirya wa ko kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262