Yaki Ya Yi Zafi, Amurka Ta Fara Neman $200bn don Ci gaba da Farmakin Iran

Yaki Ya Yi Zafi, Amurka Ta Fara Neman $200bn don Ci gaba da Farmakin Iran

  • Pentagon na neman karin kudi domin ta samu damar ci gaba da kai hare-hare a yakin da ta shigar wa Isra'ila a kan Iran
  • Rahotanni sun tababtar da cewa Amurka tana tafka mummunar asara bayan Iran ta rikakai hari kan kadarorinta a Gabas ta Tsakiya
  • Ana hasashen za a samu rikici mai zafi a majalisar dokokin Amurka saboda yawn kudin da ma'aikatar tsaron ta ke nema don ci gaba da yakin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Ma’aikatar tsaron Amurka, wato Pentagon, ta bukaci Fadar White House da ta amince da wani sabon kasafin kudi don ci gaba da yakar Iran.

A hali yanzu, Pentagon na neman kudin da ya haura Dala biliyan 200 domin ci gaba da daukar nauyin yakin Iran.

Kara karanta wannan

Gobara ta tilasta wa jirgin yakin Amurka gudu wa daga yakin Iran

Pentagon na neman karin kudin yaki da Iran
Zauren majalisar Amurka wanda ke a Washington DC. Hoto: @RepMackenzie
Source: Twitter

The Washington Post ta wallafa cewa wannan bukata na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran ‘yan majalisa za su nuna adawa mai tsanani a kan lamarin.

Ana hasashen buga muhawara a Amurka

The Jerusalem Post ta wallafa cewa za a buga muharawa a majalisar Amurka musamman wadanda ke ganin bai kamata a kara zurfafa Amurka cikin wannan rikici ba.

Wata majiya mai karfi a gwamnatin ta bayyana cewa wannan kudin ya haura abin da aka kashe a hare-haren sama da aka yi a baya-bayan nan.

An ce an tsara kudin ne domin kara samar da makamai masu muhimmanci da suka lalace a yayin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan dubunnan wurare cikin makonni uku da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jami’ai sun yi magana ne a boye saboda tsananin muhimmancin bayanan da ake tattaunawa a kai.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Gwamnati za ta mika bukata ga Majalisar Amurka

Har yanzu ba a tabbatar da adadin da Fadar White House za ta mikawa majalisa ba, amma akwai masu ganin bukatar Pentagon din ba za ta samu karbuwa cikin sauki ba.

Ana sa ran Trump zai mika bukatar Pentagon ga Majalisa
Shugaban Amurka, Donald Trump yana sanya hannu a kan wasu takardu a ofis Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

A cikin makonni biyu da suka wuce, Pentagon ta gabatar da bukatu daban-daban na kudi yayin da ta ke ci gaba da kai hare-hare sassa daban-daban a Iran.

Ana sa ran wannan bukata za ta haifar da babban rikici a majalisar dokokin Amurka, musamman ganin yadda ra’ayin jama’a bai nuna cikakken goyon baya ga yakin ba.

‘Yan jam’iyyar Democrat sun riga sun nuna adawa mai karfi, yayin da ‘yan Republican ke nuna goyon baya amma ba tare da tsayayyen tsari na yadda dokar za ta samu karbuwa ba.

Jirgin yakin Amurka ya samu matsala

A baya mun wallafa cewa jirgin ruwan yakin Amurka, USS Gerald R. Ford ya janye daga yankin Iran bayan ya samu matsala ana tsaka da kai wa kasar hari.

Kara karanta wannan

Iran ta 'ki hakura, ta taso Amurka a gaba game da kashe yan mata a makaranta

Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsala bayan gobara ta tashi a cikinsa, ta jikkata ma’aikata biyu ba tare da lalata muhimman abubuwa da dama a cikinsa.

Duk da haka, sauran jiragen rundunar na ci gaba da aiki a yankin Gabas ta Tsakiya yayain da Isra'ila da Amurka suka hada kai ana yakar Iran da hadin gwiwar Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng