Trump Ya Barranta Amurka da Harin da Isra'ila Ta Kai Wuri mai Muhimmanci a Iran

Trump Ya Barranta Amurka da Harin da Isra'ila Ta Kai Wuri mai Muhimmanci a Iran

  • Shugaban Amurka, Donald J Trump ya yi gargadi kan rikicin Gabas ta Tsakiya bayan wani harin Isra'ila da filin gas da ke Iran
  • Ya zargi Iran da kai hari kan Qatar ba tare da cikakken bayani a kan harin da aka mai wani wuri mai muhimmanci a kasarta ba
  • Ya ce Amurka za ta dauki mataki mai tsauri idan aka sake kai hari Qatar, tare da karin bayani game da mummunan harin Isra'ila

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States – Shugaban Amurka, Donald J. Trump, ya fitar da wata sanarwa mai zafi kan rikicin da ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya yi magana kan hare-haren da suka shafi Isra'ila, Iran da kuma Qatar.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta kai hari kan wani muhimmin wurin hakar gas da ake kira South Pars Gas Field da ke cikin Iran, sakamakon 'fushin' abubuwan da ke faruwa a yankin.

Trump ya musanta masaniya game da harin Isra'ila a Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Benjamin Netanyahu Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

A cikin sanarwar da ya fitar wacce Fadar White House ta wallafa a shafin X, Trump ya ce an kai harin ne a wani karamin bangare na filin gas din.

Trump ya magantu kan harin Isra'ila

A cewarsa, Amurka ba ta da masaniya kan wannan hari, kuma ba ta da hannu a ko kadan a cikin shirya wa ko kai harin.

Haka kuma, ya jaddada cewa Qatar ma ba ta da masaniya ko shiri kan abin da ya faru kafin aukuwar lamarin da ya sosa zuciyar Iran.

Trump ya zargi Iran da kai hari kan wani bangare na cibiyar gas ta Qatar ba tare da cikakken bayani ba, yana mai cewa hakan bai dace ba.

Trump ya gargaɗi Iran

Donald J Trump ya ce ya kamata a dakatar da irin wadannan hare-hare domin kauce wa kara dagula al’amura a Gabas ta Tsakiya.

Ya kara da cewa babu wani karin hari da Isra’ila za ta sake kaiwa a wannan muhimmin filin gas, sai dai idan Iran ta sake daukar matakin kai hari kan Qatar.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Trump ya yi gargadi mai tsauri cewa idan aka sake kai hari kan cibiyar gas ta Qatar, Amurka za ta dauki mataki mai tsanani..

Ya ƙara da cewa akwai yiwuwar rusa gaba daya filin gas na South Pars da karfin da Iran ba ta taba gani ba.

Trump ya yi wa Iran barazana bayan harin Isra'ila
Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila da Donald Trump Shugaban Amurka Hoto: Getty image
Source: UGC

Sai dai ya bayyana cewa ba ya son a kai ga irin wannan mummunan mataki saboda illolin da hakan zai haifar na dogon lokaci ga Iran da yankin baki daya.

Ya kammala da cewa Amurka za ta ci gaba da sa ido kan lamarin, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare muradunta da na kawayenta.

Trump ya soki NATO

A baya, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya soki ƙasashen NATO kan kin taimakawa Amurka da Isra'ila wajen yaki da ake yi da ƙasar Iran.

Donald Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar taimakon abokan hulɗarta wajen yaƙar Irane duk da matsin lamba kan farashin mai yayin da ake ci gaba da yakin

Shugaban Amurka ya nuna takaici musamman kan Birtaniya da kuma sukar tsarin haɗin gwiwar tsaro wanda ya hana Amurka samun tallafinta.

Kara karanta wannan

China ta shirya kai dauki, ta bayyana tallafin da za ta tura kasar Musulunci ta Iran

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng