Azumi Ya Zo Karshe: Daular Larabawa Ta Sanar da Ranar Hawa Idin Ƙaramar Sallah

Azumi Ya Zo Karshe: Daular Larabawa Ta Sanar da Ranar Hawa Idin Ƙaramar Sallah

  • Hadaddiyar Daular Larabawa ta ayyana Juma'a a matsayin ranar Sallah bayan da ba aka kasa ganin jairin watan Shawwal
  • Ma'aikatan gwamnati a UAE za su fara hutun Sallah daga gobe Alhamis har zuwa Lahadi, yayin da za a cika azumi 30
  • An tsara gudanar da sallar Idi a cikin masallatai maimakon filin idi a wasu matakai da ƙasar ta dauka don tsaron jama'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Dubai - Hukumomin ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun sanar da cewa Juma'a, 20 ga Maris, 2026 ita ce ranar 1 ga watan Shawwal, watau ranar idin ƙaramar Sallah.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a yau Laraba, wanda hakan ke nufin za a cika azumi guda 30 a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bayan sanarwar Saudiyya, Sarkin Musulmi ya fadi ranar da za a yi karamar Sallah a Najeriya

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ayyana Juma'a a matsayin ranar idin karamar Sallah.
An hango wata na shirin faduwa a saman masallacin Zayed da ke Abu Dhabi a ranar 14 ga Maris, 2025. Hoto: Fadel Senna/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An bada hutun Sallah a UAE

Hukumar kula da ma'aikatan tarayya (FAHR) da Ma'aikatar Kwadago sun riga sun sanar da ranakun hutu ga ma'aikatan ƙasar, a cewar rahoton Gulf News.

Rahotanni sun bayyana cewa ma'aikatan gwamnati za su tafi hutun Sallah ne daga gobe Alhamis, 19 ga Maris, har zuwa ranar Lahadi, 22 ga Maris.

Sannan, sanarwar hukumomin UAE ta bayyana cewa ma'aikata za su koma bakin aiki a ranar Litinin, 23 ga Maris bayan an gama shagulgulan Sallah.

Bayanin ganin wata a Daular Larabawa

A yau Laraba, 18 ga Maris, wadda ta dace da 29 ga watan Ramadan, kwamitocin duba wata a fadin masarautun ƙasar, ciki har da Dubai da Abu Dhabi, sun yi kokarin ganin jairin watan jim kaɗan bayan faɗuwar rana.

To sai dai, masana sararin samaniya sun bayyana cewa yanayin ganin watan a yau ba ya da kyau ko kaɗan saboda:

Kara karanta wannan

Akwai kura: Isra'ila ta sake yi wa Iran lahani, ta kashe babban Minista

  • Watan ya kasance ƙasa sosai a sararin samaniya lokacin da rana ta faɗi.
  • Hasken watan ya kasance da rauni sosai, wanda hakan ya sa ganinsa da ido ya gagara.
  • Watan ya faɗi kusan tare da rana, wanda hakan ya rage lokacin duba shi bayan sallar Magriba.

Sakamakon waɗannan dalilai, masana ilimin taurari suka sanar da cewa gobe Alhamis ne watan zai fi fitowa fili kuma ya daɗe a sararin samaniya kafin ya faɗi.

Za a gudanar da sallar Idi da misalin karfe 6:18 zuwa 6:20 a wasu sassan UAE.
Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum (na 3 daga dama a sahun gaba), Firayim Ministan Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar idi. Hoto: -/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Lokutan sallar idi a masallatan UAE

Hukumomin ƙasar sun fitar da jadawalin lokutan sallar Idi a manyan biranen ƙasar. An tsara za a gudanar da sallar ne jim kaɗan bayan fitowar rana kamar haka:

Yawancin masallatai za su tayar da sallah mintuna 15 zuwa 25 bayan fitowar rana, in ji rahoton The Sunday Guardian.

A birnin Dubai, ana sa ran fara sallar da misalin ƙarfe 6:18 zuwa 6:20 na safe, yayin da a Abu Dhabi za a fara da misalin ƙarfe 6:20 na safe.

Wani muhimmin mataki da hukumomin suka ɗauka shi ne umarnin gudanar da sallar Idi a cikin manyan masallatan da aka amince da su maimakon filayen idi domin tabbatar da tsaron jama'a.

An fadi ranar karamar Sallah a Najeriya

Kara karanta wannan

Bayan gama duban jinjirin wata, kasar Saudiyya ta sanar da ranar karamar Sallah

A wani labari, mun ruwaito cewa, Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa ba ta samu rahoton ganin jinjirin watan karamar Sallah ba a fadin Najeriya.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana cewa za a cika azumi 30, sannan a yi sallar idi ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026.

Ya kuma taya al'ummar musulmi murnar zagayowar karamar Sallah, inda ya bukaci su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Najeriya addu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com