Bidiyo: Gargadin da Ali Larijani Ya Yi wa Amurka da Isra'ila Kafin Su Kashe Shi
- Ali Larijani ya gargadi Amurka kwanaki kadan kafin kisan sa, inda ya ce shahadar shugabannin kasr Iran za ta kara wa juyin juya hali karfi
- Tsohon shugaban majalisar tsaron ya ce Amurka da Isra'ila na son tarwatsa kasar sa, amma ya ce ba abin da hakan zai faru sai kara karfi
- An kashe Larijani a harin sararin samaniya na Isra'ila bayan ya shafe shekaru yana tsara manufofin tsaro da kare tsarin mulkin addini a Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Kwanaki kaɗan kafin a kashe shi, Ali Larijani, shugaban majalisar tsaro na ƙasar Iran, ya gargaɗi Amurka da Isra'ila cewa kisan shugabannin Iran zai ƙara wa ƙasar ƙarfi ne kawai.
Gogaggen ɗan siyasar Iran, Larijani, ya kasance ɗaya daga cikin manyan mutane masu faɗa a ji a jamhuriyar Musulunci, kuma wanda ya tsara manufofin tsaro, sannan babban mai ba Ayatollah Ali Khamenei shawara.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Source: Getty Images
"Ku kashe mu, Iran ta kara karfi" - Larijani
A ranar 6 ga Maris, Larijani, mai shekaru 67 ya yi magana da tashar Al Jazeera, inda ya nanata kalaman Ali Khamenei kuma ya ce, "Shahidai ne ke sa juyin juya hali ya ƙara ƙarfi."
"Bayan harin da suka kai kan Ayatollah Khamenei, wanda kuma ya kashe wasu daga cikin kwamandojinmu. Ba wani babban jagora kamar haka da aka sake kashe wa tun lokacin.
"Kun gani, Ayatollah Khamenei, jagoran wannan ƙasa, ya yi shahada, amma mutane suna makoki cikin dakewar zuciya. Sun kara tsaya wa dakin daka da rundunar juyin juya hali.
"Yanzu, a ce sun kashe wasu mutum biyar ɗin. Sun kashe wani babban mutum kuma sun sa ya yi shahada, to sun kara farkar da mutanenmu ne. Wannan shi ne abin da Imam (Khamenei) ya saba faɗa game da shahadar Farfesa (Morteza) Motahari: 'Shahidai ne ke sa juyin juya hali ya ƙara ƙarfi.
"Kuna kashe mu, al'ummar Iran ta na daɗa zabura ne."
- Ali Larijani.
Gargaɗin Larijani ga Trump
A makon da ya gabata, Times Magazine ta rahoto cewa Larijani ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump da ya "kiyayi kansa – kada a kawar da kai".
An yi wa Larijani ganin ƙarshe a titunan Tehran a ranar Juma'a, 13 ga Maris yayin wani taro na bikin ranar Kudus domin nuna goyon baya ga Falasdinu.
"A fili yake cewa ƙarfinsu ya fara ƙarewa," Larijani ya shaida wa wani d'an jarida yayin da yake tsokaci kan shirin Amurka na "Operation Epic Fury.
Ya kara da cewa:
"Matsalar Trump ita ce ya kasa fahimtar cewa al'ummar Iran sun kai makurar da a yanzu ba abin da ke ba su tsoro, kuma sun ƙudiri aniyar dogewa kan manufarsu."

Source: Getty Images
Mutuwar Ali Larijani
Ali Larijani, ɗan shekara 67, wanda Isra'ila ta kira shugaban Iran na zahiri bayan rasuwar Khamenei, ya mutu ne a wani harin sama na Isra'ila, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran suka tabbatar.

Kara karanta wannan
Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi
Ana kallon Larijani a matsayin mai hikima da sanin dabaru amma koyaushe yana tsaye daram domin kare tsarin mulkin addini na Iran, in ji rahoton NDTV.
Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya hali ne a lokacin yaƙin Iran da Iraki, ya zama shugaban gidan rediyo da talabijin na ƙasa kafin ya gudanar da ayyuka a majalisar tsaro na ƙasa a ɓangarorin biyu na kasancewarsa ɗan majalisa, inda ya kasance kakakin majalisa na tsawon shekaru 12.
Kalli bidiyon hirar da aka yi da shi a nan kasa:
Isra'ila ta kashe Gholamreza Soleimani
A wani labari, mun ruwaito cewa, IRGC ta sanar da kisan daya daga cikin manyan kusoshinta, Birgediya Janar Gholamreza Soleimani, wanda shi ne shugaban dakarun sa-kai na Basij.
Sanarwar, wadda aka fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa Janar Soleimani ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon wani hari na Amurka da Isra'ila.
Baya ga kisan Soleimani, Gwamnatin Iran ta kuma tabbatar da wani babban rashi a safiyar yau Laraba, inda aka sanar da kisan Ali Larijani, shugaban majalisar tsaro.
Asali: Legit.ng
