Kamar Iran, an Samu Kasar da za Ta Gwabza da Amurka bayan Barazanar Trump
- Shugaban kasar Cuba ya yi magana mai kaushi ga shugaba Donald Trump na Amurka bayan dawo da wutar lantarki da ta dauke a kasar shi
- Miguel Díaz-Canel ya ce yana daidai da Shugaban Amurka idan ya yi niyyar shiga kasar su bayan barazanar da ya musu kwananan nan
- Donald Trump da wasu manyan jami'an gwamnatinsa sun sha maganganu da ke nuna alamun suna son kwace kasar Cuba a baya bayan nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Cuba - Rahotanni sun nuna cewa an fara musayar yawu tsakanin Shugaba Donald Trump da shugaban kasar Cuba, Miguel Díaz-Canel.
Tun a kwanakin baya gwamnatin Amurka ta kakabawa Cuba takunkumi tare da barazanar kutsawa kasar a lokuta daban-daban.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta gano cewa shugaba Miguel Díaz-Canel ya wallafa martani ga Donald Trump ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Iran ta sake jikawa Amurka aiki, ta ruguza shirin Shugaba Trump ana tsaka da musayar wuta
Martanin kasar Cuba ga Donald Trump
Shugaba Miguel Díaz-Canel ya bayyana cewa Duk wani yunkuri daga Amurka na karbe iko da Cuba zai gamu da turjiya mai karfi.
Tashar CNN ta wallafa cewa shugaba Miguel Díaz-Canel ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin da wutar lantarki ta fara dawowa a wasu sassan kasar bayan lalacewar tushen lantarki a fadin kasar.
Díaz-Canel ya ce gwamnatocin Amurka daban-daban sun shafe sama da shekaru 60 suna kokarin ware Cuba, inda ya zargi Washington da amfani da raunin tattalin arzikin kasar a matsayin dalilin neman kwace ikonta.
Ya ce:
“Ta haka ne kadai za a iya bayyana mummunan yakin tattalin arziki da ake yi, wanda ake amfani da shi a matsayin horo ga daukacin al’umma.”
Ya kara da cewa:
“A ko wane hali, Cuba na da tabbacin cewa duk wani mai kai hari daga waje zai gamu da turjiya mai karfi.”
Maganar Shugaba Trump kan Cuba
Rahotanni sun nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sha yin barazana ga shugabannin Cuba da cewa zai karbe ikon kasar.
Bayan ya bayyana a ranar Litinin cewa zai iya yin duk abin da ya ga dama da Cuba, a ranar Talata, Trump ya sake cewa:
“Ba da jimawa ba za mu dauki wani mataki kan Cuba.”

Source: Getty Images
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya kara da cewa Cuba na bukatar sababbin shugabanni. Inda ya ce:
“Tattalin arzikinsu ba ya aiki…suna cikin matsala mai tsanani, kuma shugabannin da ke kan mulki ba su san yadda za su gyara ba, don haka dole ne a samu sababbin shugabanni.”
Sultan ya soki Amurka da Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana game da yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran.
Ya bayyana cewa harin ya saba dokar kasa da kasa kuma Iran da na damar kare kanta kamar yadda dokokin majalisar dinkin duniya suka tanada.
Sultan ya kara da cewa akwai rashin adalci a kan yadda majalisar dinkin duniya ta soki Iran kan toshe mashigar Hormuz ba tare da sukar Amurka da Isra'ila ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
