Trump Ya Soki NATO, Ya Yi Magana game da Ƙasashen da Suka Ki Taya Su Yaƙar Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya soki ƙasashen NATO kan kin taimakawa Amurka da Isra'ila wajen yaki da ake yi da Iran
- Donald Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar taimakon abokan hulɗarta wajen yaƙar Irane duk da matsin lamba kan farashin mai
- Ya nuna takaici musamman kan Birtaniya da kuma sukar tsarin haɗin gwiwar tsaro wanda ya hana Amurka samun tallafinta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi ƙasashen kawancen tsaro na NATO da aikata babban kuskure da wauta.
Ya bayyana takaicinsa bayan kasashen sun ki taimakawa Amurka wajen kare mashigar ruwa ta Hormuz yayin rikicin da ke tsakaninta da Iran.

Source: Twitter
BBC News ta ruwaito Trump ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Firaministan Ireland, Micheál Martin, a Fadar White House.

Kara karanta wannan
Hormuz: Kasashen Turai sun yanke shawara kan abin da Amurka ta nema a yakinta da Iran
Nato ta fusata Trump
France 24 ta ruwaito cewa Trump ya ce yawancin ƙasashen NATO sun nuna ba sa son shiga wannan yaƙi, wanda wasu daga cikinsu ke kallon sa a matsayin wanda bai dace ba. Duk da matsin lamba da rikicin ya haifar kan farashin mai a duniya saboda mashigar Hormuz, Trump ya dage cewa Amurka za ta iya tafiyar da al’amura ba tare da taimakon kowa ba.

Source: Getty Images
A cewarsa, wasu ƙasashe na iya taimakawa wajen rakiyar jiragen ruwa a yankin, amma bai bayyana sunayensu a bainar jama’a ba.
A wata tattaunawa mai zafi a ofishinsa, ya jaddada cewa:
"Ba mu buƙatar wani taimako.” Sai dai ya ƙara da cewa da ya dace abokan hulɗa au kasance masu goyon bayan Amurka.
Trump ya caccaki Birtaniya
Trump ya nuna cewa rashin son tura jiragen kwashe bama-bamai a yankin Tekun Gulf daga ƙasashen NATO ba wani babban al’amari ba ne, amma ya kira hakan da rashin adalci ga Amurka. Ya fi mayar da hankali wajen sukar Birtaniya, yana mai cewa ƙasar ba ta taka rawar gani ba wajen kai hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran.
Shugaban ya ce dangantakar Amurka da Birtaniya ta kasance mai ƙarfi a baya, amma ta samu tangarda tun bayan zuwan Firaminista Keir Starmer.
Ya kuma bayyana wannan yaƙi a matsayin wata babbar jarabawa ga dangantakar Amurka da abokan hulɗarta.
Duk da haka, lokacin da aka tambaye shi ko zai ɗauki matakin ramuwar gayya kan ƙasashen da ba su goyi bayan Amurka ba, Trump ya ce babu wani shiri a halin yanzu. Haka kuma, Trump ya koka cewa ƙasashen NATO sun amfana da biliyoyin Daloli daga tallafin Amurka ga Ukraine a yaƙinta da Russia. Ya ce Amurka na kare abokan hulɗarta, amma su ba sa nuna irin wannan goyon baya a lokacin da take buƙata ba, musamman a irin wannan yanayi na rikici.
Iran za ta nemi diyya daga Trump
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta bayyana cewa ta za ta taba manta wa da harin da Amurka ta kai kan dalibanta a ranar farko na yakin da suka jawo ba.
A wannan mummunan hari da ya tayar da hankulan jama'a fiye da dalibai 160 ne suka rasu bayan Amurka da Isra'ila sun jefa bam a kan makarantar.
Duk da Shugaban Amurka Donlad Trump ya sha musanta zargin sun tafka danyen aiki, bincike ya tabbatar da cewa hare-haren Amurka ne suka kashe yaran.
Asali: Legit.ng
