Bayan Kashe Manyan Jagorori 2 a Iran, Isra'ila Ta Fadi Shirinta kan Mojtaba Khamenei

Bayan Kashe Manyan Jagorori 2 a Iran, Isra'ila Ta Fadi Shirinta kan Mojtaba Khamenei

  • Hare-haren da Isra'ila ta kai sun yi sanadiyyar kashe shugaban majalisar tsaron Iran da babban kwamandan dakarun Basij
  • Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa za ta ci gaba da farmakar jami'an gwamnatin Iran yayin da ake ci gaba da gwabza fada
  • Ta bayyana cewa ba ta san inda sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, yake ba amma za ta farauto shi domin raba shi da duniya

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta bayyana cewa ta kashe shugaban majalisar tsaron Iran, Ali Larijani da babban kwamandan dakarun Basij, Gholamreza Soleimani.

Rundunar IDF ta kuma bayyana cewa za ta farauto tare da kashe sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei.

Isra'ila na son kashe Mojtaba Khamenei
Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Hamed Jafarnejad
Source: Getty Images

Jaridar The Times of Israel ta ce kakakin rundunar IDF, Birgediya Janar Effie Defrin, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 17 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Mene ne shirin Isra'ila ka Mojtaba Khamenei?

Birgediya Effie Defrin ya sha alwashin cewa sojoji za su farauto sabon Jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei.

"Muna kai hari ga dukkan shugabannin gwamnatin Iran, kamar yadda aka gani a ranar da ta gabata."
“Ba mu san komai game da Mojtaba Khamenei ba, ba mu jin muryarsa, ba mu ganinsa, amma zan iya gaya muku abu ɗaya: za mu bi sawunsa, mu gano shi, sannan mu kashe shi."
"Za mu ci gaba, kamar yadda muka tabbatar, za mu ci gaba da bin duk wanda ke barazana ga kasar Isra'ila ko kuma ya ɗaga hannu a kanta."
“Ba shi da kariya. Za mu bi shi, mu gano shi, mu kuma kashe shi."

- Birgediya Janar Effie Defrin

An tabbatar da kashe Larijani, Gholamreza

Tashar Aljazeera ta ce shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya kira Gholamreza Soleimani da "fitaccen janar" kuma ya ce ya "samu matsayin shahada a yaƙi da mafi munanan makiya bil'adama", tare da mataimakinsa da wasu wasu sojoji kalilan.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Isra'ila ta kashe babban kwamanda a Iran

Isra'ila ta yi wa Iran barna
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa, majalisar tsaro ta ƙasar Iran ta tabbatar da kisan Ali Larijani, bayan da Isra'ila ta yi iƙirarin kashe shi a wasu hare-hare da aka tsara.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Bayan rayuwar da ya shafe yana fafutukar ɗaukaka Iran da Juyin Juya Halin Musulunci, a ƙarshe ya kai ga babban burinsa da ya daɗe yana fatan samu, ya amsa kiran gaskiya, kuma ya sami babban matsayi na shahada a fagen hidima cikin alfahari."

Iran ta aika sako ga kasashen Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban majalisar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ali Larijani, ya fitar da wani saƙo zuwa ga Musulmin duniya baki ɗaya da kuma gwamnatocin ƙasashen Musulmi.

Ali Larijani ya yi kiran hadin kai tare da sukar abin da ya bayyana a matsayin cin zarafi daga Amurka da Isra’ila a kan Iran.

Jami’in na Iran ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin rashin nuna goyon baya daga yawancin ƙasashen Musulmi yayin fafatawar da ake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng