Kungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam Ta Tsoma Baki game da Harin Iran kan Kasashen Larabawa
- Iran ta kaddamar da hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami a kasashen Larabawa da ke makwabtaka da ita
- Hakan ya biyo bayan harin da Isra'ila ta kai mata wanda ta mayar da martani kan sansanonin sojojin Amurka domin daukar fansa
- Sai dai kungiyar kare hakkin dan Adam da HRW ta ce hakan na barazana ga rayukan fararen hula da ba su da alhakin komai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kungiyar kare hakkin bil’adama ta 'Human Rights Watch' ta yi magana kan harin Iran a kasashen Larabawa.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da hare-haren inda ta ce hakan ya saba ka’ida, kuma ya jefa rayukan fararen hula cikin hadari sosai.

Source: Getty Images
Harin da Iran ta kai yankin Gulf
Tun bayan da hare-haren Amurka da Isra’ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta harba daruruwan jirage marasa matuka da makamai masu linzami kan wuraren sojojin Amurka, cewar kungiyar HRW a shafinta.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka
Iran ta bayyana cewa tana kai hare-haren ne kan sansanonin soja da muhimman kayayyakin more rayuwa a kasashen kungiyar GCC a yankin Gulf.
Sai dai kungiyar ta ce da dama daga cikin hare-haren Iran sun afkawa gidajen zama, otel, filayen jiragen sama na farar hula da kuma ofisoshin jakadanci.
Harin Iran: Matsalar da kungiyar HRW ta hango
Kungiyar ta kara da cewa an kai hare-haren har kan cibiyoyin hada-hadar kudi, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa da ke kare fararen hula.
Ya zuwa ranar Litinin, an samu mutuwar akalla fararen hula 11, yayin da mutane 268 suka jikkata sakamakon hare-haren, galibinsu bakin haure ne.
Rahoton ya ce wannan bayanin ya fito ne daga majiyoyin gwamnatocin kasashen GCC da abin ya shafa a yankin.

Source: Facebook
Shugaban Iran ya nemi afuwar kasashen Larabawa
A ranar 8 ga watan Maris, 2026, shugaban Iran ya nemi afuwa kan hare-haren da aka kai a kasashen Gulf, amma duk da haka hare-haren sun ci gaba.
“Fararen hula, musamman bakin haure, na fuskantar barazana, ana kashe su tare da jikkata su sakamakon hare-haren Iran."

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
- Joey Shea.
Ta bayyana cewa wadannan hare-hare na kara jefa mutane cikin hadari a kasashen Saudi Arabia da UAE da ke yankin Gulf, cewar rahoton Al Jazeera.
A gefe guda kuma, hare-haren Amurka da Isra’ila a cikin Iran sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 1,444 tare da jikkata fiye da 18,500.
Iran ta tura sako ga kasashen Musulmi
Kun ba ku labarin cewa yaki na ci gaba da gudana tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wani babban jami'i a gwamnatin Iran, Ali Larijani, ya aika da sako ga kasashen Musulmi kan yakin da ake yi tsakanin kasarsa da kuma Isra'ila.
Ali Larijani ya koka kan yadda Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran yayin da ake tsaka da tattaunawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng