Shin da Gaske an Tafi da Mojtaba Khamenei zuwa Rasha Don Jinya? An Ji Gaskiyar Zance

Shin da Gaske an Tafi da Mojtaba Khamenei zuwa Rasha Don Jinya? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wasu rahotanni da ke nuna cewa an fitar da sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, zuwa Rasha don duba lafiyarsa
  • Rahotannin sun yi ikirarin cewa an fitar da Mojtaba ne domin ya yi jinya sakamakon raunukan da ya samu a wasu hare-hare da aka kai
  • Jakadan Iran a kasar Rasha, Kazem Jalali, ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ake ta yadawa kan lafiyar Mojtaba Khamenei

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Ana ta yada jita-jita kan lafiyar sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei.

Jita-jitar dai na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce game da inda sabon jagoran addinin na Iran da yake bayan da aka ce ya ji rauni.

An yada jita-jita kan lafiyar Mojtaba Khamenei
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Rouhollah Vahdati
Source: Getty Images

An yada jita-jita kan Mojtaba Khamenei

Shafin Firspost ya ce rahoton baya-bayan nan ya yi iƙirarin cewa Khamenei yana Moscow kuma yana buƙatar tiyata biyo bayan harin Amurka mai suna Operation Epic Fury.

Kara karanta wannan

Ana rade radin ya mutu, Jagoran addinin Iran ya yi nadin da zai iya rikita Amurka da Isra'ila

An ce a halin yanzu yana karɓar magani ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke da alaƙa da ɗaya daga cikin gidajen Shugaban Rasha Vladimir Putin.

Rahotannin sun kuma nuna cewa Khamenei kamar bai san ma ana tsaka da yaƙi ba, ko kuma shi ne sabon shugaban Iran.

Me hukumomi a kasar Iran suka ce?

Tashar Aljazeera ta ce jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya musanta rahoton kafofin yaɗa labarai na cewa sabon Jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, yana karɓar magani a Moscow.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya bayyana cewa Mojtaba Khamenei yana cikin ƙoshin lafiya kuma nan ba da jimawa ba zai gabatar da jawabi.

"Zan iya gaya muku cewa yana nan lafiya. Kun riga kun ji labarin jawabin nasa, kuma ina fatan nan ba da jimawa ba zai gabatar da wani jawabin ga jama'a."

- Esmaeil Baqaei

Ya nuna cewa rikicin da ke Gabas ta Tsakiya yaƙi ne da Amurka da Isra'ila suka ɗora wa Iran.

"Al'ummar Iran sun ƙuduri niyyar kare ƙasarsu, kuma abin da muke yi ke nan a yanzu."

Kara karanta wannan

An sanar da yanayin da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ke ciki bayan kai masa hari

- Esmaeil Baqaei

Ana ta yada jita-jita kan rashin lafiyar Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei, sabon jagoran addini na kasar Iran Hoto: Hamed Jafarnejad
Source: Getty Images

Abin da Rasha ta ce kan lamarin?

Tashar TASS News Agency ta ce sakataren yaɗa labarai na fadar shugaban Rasha, Dmitry Peskov, ya ƙi yin sharhi kan zargin cewa sabon jagoran na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya isa Moscow don neman magani.

"Ba mu taɓa yin sharhi kan irin waɗannan rahotannin."

- Dmitry Peskov

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Iran, sabon jagoran addinin ya ji rauni ne a hare-haren Amurka da Isra'ila amma an bayar da rahoton cewa yana jin sauƙi a halin yanzu.

Mojtaba Khamenei ya yi nadin mukami

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya fara nada mutanen da za su taimaka masa wajen gudanar da mulki.

Mojtaba Khamenei, ya naɗa tsohon shugaban rundunar Juyin Juya Hali (IRGC), Mohsen Rezaei, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin sojoji.

Nadin na zuwa ne yayin da Amurka da Isra'ila suka yi ikirarin illata Mojtaba Khamenei, inda aka ji Shugaba Donald Trump na cewa babu tabbacin yana raye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng