Abin Boye Ya Fito; Gargadin da Aka Yi Wa Trump kafin Fara Yaki da Iran

Abin Boye Ya Fito; Gargadin da Aka Yi Wa Trump kafin Fara Yaki da Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya samu gargadi kan abin da zai iya faruwa idan aka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an sanar da shugaban na Amurka cewa akwai abubuwan da Iran za ta iya yi muddin aka kai mata hari
  • Daga cikin abin da aka sanar da Trump shi ne Iran za ta iya rufe mashigar ruwa ta Hormuz wadda ke da matukar muhimmanci wajen jigilar kayan makamashi

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - An yi wa Shugaba Donald Trump gargaɗin cewa kai wa Iran hari na iya janyo ramuwar gayya ga kasashen Gulf da ke ƙawance da Amurka.

Hakan na zuwa ne duk da iƙirarin da ya yi a ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026 cewa martanin na Tehran ya zo ne a matsayin mamaki.

Kara karanta wannan

Iran ta sake jikawa Amurka aiki, ta ruguza shirin Shugaba Trump ana tsaka da musayar wuta

An ja kunnen Trump kafin kai hari a Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Tashar Reuters ta ce wani jami’in Amurka da wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan rahotannin sirrin Amurka suka sanar mata da hakan.

Wane gargadi aka yi wa Trump?

Majiyoyin wadanda suka tabbatar da gargadin da aka yi wa Trump duk sun nemi a sakaya sunayensu.

Ƙididdigar bayanan sirri na kafin yaƙi ba su ce lallai martanin Iran zai faru ba, amma tabbas yana cikin jerin sakamakon da ake sa ran za su iya faruwa.

Wasu ƙarin majiyoyi biyu sun bayyana cewa an kuma yi wa Trump gargaɗin cewa Iran na iya ƙoƙarin rufe mashigar Hormuz, wadda babbar hanyar jigilar man fetur ce ga duniya, jaridar Business Standard ta kawo labarin.

Trump ya bayyana har sau biyu a ranar Litinin cewa hare-haren fansar da Iran ta kai kan Qatar, Saudi Arabia, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain, da Kuwait ba a yi tsammaninsu ba.

An kuma bayar da rahoton cewa an gargaɗi Shugaban tun kafin a fara harin cewa Iran za ta iya ƙoƙarin rufe Mashigar Hormuz mai matuƙar mahimmanci, matakin da zai sami gagarumin tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Kara karanta wannan

'Ba Amurka ba ce,' an gano kasa 1 da take da makullin bude kasuwar mai ta duniya

An yi wa Trump gargadi kafin kai hari a Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Trump ya yi mamakin martanin Iran

Duk da waɗannan gargaɗin, Trump ya nace cewa ba a yi tsammanin ramuwar gayyar ba.

A ranar Litinin, lokacin da aka tambaye shi ko an ba shi bayanin sirri game da haɗarin cewa Iran za ta iya kai hari ga ƙasashen Gulf, ya yi watsi da batun.

"Ba a yi tsammanin za su farmaki duk waɗannan sauran ƙasashe na Gabas ta Tsakiya ba. Babu wanda ya yi tsammanin hakan. Mun girgiza."

- Donald Trump

Iran ta sha alwashi kan Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan rundunar sojojin ruwan Iran, Rear Admiral Shahrami Irani, ya sha alwashi kan kasar Amurka.

Rear Admiral Shahrami Irani ya bayyana cewa makiya Iran za su fuskanci martani mai zafi sakamakon kisan aƙalla sojojin ruwa 87 a kusa da gabar Sri Lanka da ke tekun Indiya.

Babban kwamandan bayyana cewa al'ummar ƙasar na cikin baƙin ciki sakamakon wannan babban rashi, amma ya jaddada ƙudurin sojojin Iran na ganin sun ɗauki fansar jinin shahidan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng