"Mun Girgiza": Trump Ya Fadi Abin da Ya Ba Shi Mamaki a Yaki da Iran

"Mun Girgiza": Trump Ya Fadi Abin da Ya Ba Shi Mamaki a Yaki da Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin tsokaci kan yakin da ake yi tsakanin kasarsa, Isra'ila da Iran
  • Donald Trump ya bayyana cewa ya yi mamakin abin da ya gani daga wajen Iran a yakin da ake yi wanda aka fara a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026
  • Shugaban na Amurka ya bayyana cewa bai samu bayanan sirri ba da ke nuna cewa Iran za ta kai hare-haren daukar fansa ga kasashe makwabtanta ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan hare-haren daukar fansa da Iran ta kai kan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana cewa hare-haren kan ƙasashe maƙwabta da ke ɗauke da sansanonin sojin Amurka sun zo wa Washington a matsayin “mamaki,” inda ya yi iƙirarin cewa babu wanda ya yi tsammanin irin wannan matakin.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya samu bayani, an kashe shugabannin kasar Musulunci ta Iran

Trump ya yi mamakin hare-haren Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Tashar CNN ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026.

Me ya ba Trump mamaki a yaki da Iran?

Trump ya bayyana mamakinsa game da hare-haren fansar da Iran ta kai wa ƙasashen yankin Gulf da ke kewaye da ita.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya yi mamakin yadda ba a ba shi bayanin sirri cewa Iran za ta iya kai hari ga ƙasashe maƙwabta ba, Trump ya bayyana cewa:

“A’a, kwararru mafi girma, babu wanda ya yi tunanin za su kai hari. Su, ba zan kira su ƙasashe masu kawance ba. Sun kasance kamar tsaka-tsaki ne. Sun zauna tare da su tsawon shekaru.”
"Ba a yi tsammanin za su farmaki duk waɗannan sauran ƙasashe na Gabas ta Tsakiya ba. Babu wanda ya yi tsammanin hakan. Mun gizgiza."

Trump ya bayyana cewa ƙasashen na Gulf a matsayin waɗanda mafi yawancinsu ke zaune “lafiya” a dangantakarsu da Iran, jaridar Haaretz ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Kasashe 5 da za su iya shiga cikin yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Ana yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran

Amurka, tare da haɗin gwiwar Isra’ila, sun ƙaddamar da gagarumin yaƙi a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, inda suka farmaki muhimman wuraren ayyukan soji da na gwamnati tare da kashe manyan shugabannin ƙasar, ciki har da Ayatollah Ali Khamenei.

Trump ya nuna mamakinsa kan yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba daruruwan makamai masu linzami a sansanonin Amurka da wuraren dabarun yaƙi a faɗin yankin Gulf, wani mataki da Tehran ta riga ta yi gargaɗin za ta ɗauka idan Amurka ta kai mata hari.

Iran ta ƙaddamar da hare-haren fansa a ƙasashe da dama a Gabas ta Tsakiya, ciki har da Qatar, Saudi Arabia, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain, da Kuwait.

Shugabar ma'aikatan White House ta kamu da cuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabar ma'aikatan fadar White House, Susie Wiles, ta kamu da cutar kansa.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, bayyana cewa an gano Susie Wiles tana ɗauke da cutar kansar nono a matakin farko.

Trump ya bayyana cewa shugabar ma'aikatan ta fadar White House tana cikin yanayi mai kyau kuma za ta ci gaba da gudanar da aikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng