Ba Boye Boye: Amurka Ta Fadi Yadda Iran Ta Ragargaji Sojojinta Sama da 200
- Ana cigaba da samun bayani game da irin barnar da dakarun juyin juya hali na Iran suka yi wa sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya
- Bayan kashe wasu dakarun Amurka, wani rahoto ya nuna cewa sama da sojoji 200 da Doanld Trump ya tura yaki aka raunata
- An samu bayanin ne bayan shiga mako na uku da fara yakin da Donald Trump da Benjamin Netanyahu suka kaddamar a Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rundunar sojin Amurka ta sanar da yadda dakarun Iran suka ragargaji sojojinta a kasashen Gabas ta Tsakiya a yakin da suke.
Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Donald Trump ke ikirarin cewa ya gama da Iran, ya rage karfinta na kai hare-hare kan kadarorin Amurka.

Source: Facebook
Rahoton da tashar TRT ta wallafa ya nuna cewa wani daga cikin kwamandojin rundunar sojin Amurka ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida.
Iran ta jikkata sojojin Amurka 200
Rundunar CENTCOM ta Amurka ta bayyana cewa yawan sojojinta da suka jikkata a yakin Amurka/Isra’ila da Iran ya haura 200.
Kimanin sojojin Amurka 200 ne suka samu raunuka a kasashe bakwai na yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan fara yakin, a cewar kakakin rundunar, Kyaftin Tim Hawkins.
“Yawancin wadannan raunuka ba su da tsanani, kuma sama da sojoji 180 sun riga sun koma bakin aiki,”
Inji shi, yana mai karawa da cewa:
“Sojoji 10 ne aka ware a matsayin wadanda suka samu munanan raunuka.”
Kasashen da aka kai hari kan Amurka
Ya kara da cewa an samu wadannan raunuka ne a kasashen Bahrain, Iraq, Isra’ila, Jordan, Kuwait, Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Yawan sojojin Amurka da suka jikkata a wannan yaki yanzu ya wuce 200, a cewar Hawkins, wanda ya bayar da cikakken bayani mafi zurfi zuwa yanzu kan yadda rikicin ya shafi sojojin Amurka.

Kara karanta wannan
Iran ta shiga matsala: Bataliyar sojojin Amurka mai hatsari ta bar Japan zuwa Gabas
A baya, ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta ce kimanin sojoji 140 ne suka jikkata zuwa ranar 10 ga Maris na shekarar 2026.
Yadda ake rikici tsakanin Iran da Amurka
Sojojin Amurka da Isra’ila sun kaddamar da yaki kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, lamarin da ya jawo mutuwar Ayatollah Ali Khamenei.
Tehran ta mayar da martani da jerin hare-haren makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marasa matuka, wadanda suka kai hari kan kasashen yankin da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.
Sojoji sun samu raunuka yayin da Iran ke kai wadannan hare-hare kan wuraren da sojojin Amurka ke da su da sauran muhimman wurare a yankin, a matsayin martani ga harin da aka kai mata.

Source: Twitter
Rikicin ya kuma yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka. Zuwa yanzu, sojoji 13 sun mutu, ciki har da bakwai da suka rasu sakamakon hare-hare.
Trump ya gargadi kasashen NATO
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya matsa lamba kan samun agaji daga shugabannin kasashen NATO a yaki da Iran.

Kara karanta wannan
Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya
Donald Trump ya bukaci kasashen da su hada kai su tura jiragen ruwa domin yakar dakarun Iran da suka toshe mashigar Hormuz.
Biyo bayan samun rashin goyon baya, shugaban kasar fara gargadin su game da abin da zai iya biyo baya yana mai cewa karshensu ba zai yi kyau ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
