Ana Rade Radin Ya Mutu, Jagoran Addinin Iran Ya Yi Nadin da Zai Iya Rikita Amurka da Isra'ila

Ana Rade Radin Ya Mutu, Jagoran Addinin Iran Ya Yi Nadin da Zai Iya Rikita Amurka da Isra'ila

  • Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya nada Mohsen Rezaei, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin sojoji
  • Wannan nadi na zuwa ne yayin da Amurka da Isra'ila suka yi ikirarin cewa sun raunata Mojtaba, inda suka ce ba tabbacin yana raye
  • Rezaei, mai shekaru 71 da haihuwa ya taba zama shugaban rundunar juyin juya halin Iran watau IRGC, kuma ya rike mukamai daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei ya fara nade-naden mutanen da za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulki.

Mojtaba Khamenei, ya naɗa tsohon shugaban rundunar Juyin Juya Hali (IRGC), Mohsen Rezaei, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin soji.

Mijtaba Khamenei.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta tabbatar da wannan jadi da jagoran Iran ya yi a wani rahoto da ta wallafa shafin X yau Litinin, 16 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Shugabanni a Amurka sun fadawa Trump masifar da ke tunkaro duniya

Jagoran Iran ya yi muhimmin nadi

Rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun tabbatar da cewa an yi wannan naɗi ne bisa umarnin sabon babban kwamandan rundunar sojin ƙasar.

Wannan mataki na zuwa ane yayin da Amurka da Isra'ila suka yi ikirarin illata Mojtaba Khamenei, inda aka ji Shugaba Donald Trump na cewa babu tabbacin yana raye.

Sanarwar ta ce:

“An naɗa Janar Mohsen Rezaei a matsayin mai ba da shawara kan harkokin soji bisa umarnin babban kwamanda kuma jagora na kasa, Ayatollah Mojtaba Khamenei.”

Wanene Mohsen Rezaei?

Rezaei mai shekaru 71 ya taba zama shugaban rundunar IRGC, wacce ake ɗauka a matsayin bangaren akida na rundunar sojin Iran kuma tana da babban tasiri a harkokin tsaro da siyasar ƙasar.

Bayan saukarsa daga shugabancin rundunar, ya rike mukamai daban-daban a cikin gwamnatin Iran, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yadda aka samu sauyin jagoranci a Iran

Mojtaba Khamenei mai shekaru 56 ya karɓi mulki ne a farkon wannan watan bayan mutuwar mahaifinsa, tsohon jagoran Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

An sanar da yanayin da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ke ciki bayan kai masa hari

A zamanin Ali Khamaenei, Yahya Rahim Safavi ne ke rike da mukamin mai ba da shawara kan harkokin soji. Sai dai har yanzu ba a tabbatar ba ko zai ci gaba da rike wannan matsayi a karkashin Mojtaba Khamenei

Khamenei.
Jagoran Iran, Mijtaba Khamenei da marigayi mahaifinsa, Ali Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Mojtaba Khamenei ya umarci dukkan jami’ai da shugabannin hukumomi da mahaifinsa ya naɗa da su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda aka saba.

An kama yan leken asiri 500 a Iran

A wani labarin, kun ji cewa dakarun 'yan sandan kasar Iran sun damke mutane kimanin 500 da ake zargin da yi wa Amurka da Isra'ila leken asiri.

Yan sandan sun ce kusan rabin mutanen da aka kama suna da hannu a manyan laifuffuka, ciki har da ba da bayanan wuraren da ake kai hare- hare a Iran.

Hukumar leƙen asiri ta rundunar sojojin juyin juya hali na Iran ta ce Isra’ila da Amurka na ƙoƙarin tayar da tarzoma da amfani da ‘yan leƙen asiri domin haddasa rikici a cikin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262