Ana Batun Azumi 30, Kasar Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa game da Ranar Karamar Sallah
- Saudiyya ta bukaci musulmi su fara duban jinjirin watan Shawwal daga yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan, 1447AH
- A wata sanarwa da masarautar Saudiyya ta fitar, ta ce sakamakon ganin watan ne zai tantance ranar da za a yi idin karamar Sallah ta bana
- Tuni dai masana ilimin taurari suka fara hasashen ranar da za a yi Sallah, wacce ke nuna karshen watan azumin Ramadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Yayin da watan azumin Ramadan ya fara bakwana, Saudiyya ta fitar da sanarwa ga daukacin musulmin kasar game da duban jinjirin watan Shawwal, 1447AH.
Saudiyya ta bukaci musulmin kasar su fita duba jinjirin watan karamar Sallah, wata na 10 a jerin watanni musulunci daga ranar Laraba, 29 ga Ramadan, 1447, daidai da 18 ga Maris, 2026.

Kara karanta wannan
Tarihi: Musulmi za su samu hutun ranakun salla a Amurka bayan kudirin ɗan majalisa

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shafin hukumar kula da masallatai masu alfarma na Makkah da Madinah, Inside The Haramain, ya wallafa a shafinsa na X.
Saudiyya dai ta fara azumin Ramadan na bana a tare da Najeriya, kuma yau Litinin, 16 ga watan Maris, 2025 ya zo daidai da 27 ga watan Ramadan na shekarar 1447 bayan Hijira.
Yaushe za a yi karamar Sallah a Saudiyya?
A sanarwar da Saudiyya ta fitar, ta ce sakamakon duba jinjirin watan da za yi a ranar Laraba mai zuwa ne zai tabbatar da ranar idin karamar Sallah (Eid al‑Fitr) wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan.
Sanarwar ta nuna cewa idan aka ga jinjirin watan Shawwal a wannan rana, to washegari ranar Alhamis, 19 ga watanaris, 2026 ne za a gudanar da Sallar Idi.
Sai dai idan ba a ga jinjirin watan ba ba, to za a cika azumin Ramadan zuwa kwana 30, sannan a gudanar da bikin Sallah a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026.
Za a fara duban wata a Saudiyya
Hukumomim Saudiyya sun kuma yi kira ga duk wanda ya ga jinjirin watan da idonsa ko ta hanyar na’ura, da ya garzaya kotu mafi kusa domin bada shaida.
Sanarwar ta ce:
"Masarautar Saudiyya na kira ga daukacin al'ummar musulmi da su fara duban jinjirin watam Shawwan a yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan 1447 AH daidai da 18 ga watan Maris 2026.
"Sakamakon ganin watan zai tantance ranar za a yi idin karamar sallah watau Eid Al Fitr."

Source: Twitter
Wannan na zuwa ne yayin da masana ilimin tsaurari suka yi hasashen cewa watan azumin Ramadan zai cika 30 cif a bana saboda sai asubahin ranar Alhamis za a halicci jinjirin watan Shawwal.
Sarkin Musulmi ya yi nasiha a karshen Ramadan
A wani rahoton, kun ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci musulmi su dage da addu'o'i da sadaka a goman karshe ta watan Ramadan.
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa mai daike da sa hannun sakatarenta na kasa, Farfesa Khalid Aliyu.
Sanarwar ta ce ya kamata Musulmi su shimfida ayyukan alheri ta hanyar ciyarwa da bayar da sadaka ga matalauta, marayu, gajiyayyu, da nakasassu.
Asali: Legit.ng

