Iran Ta 'Ki Hakura, Ta Taso Amurka a gaba game da Kashe Yan mata a Makaranta

Iran Ta 'Ki Hakura, Ta Taso Amurka a gaba game da Kashe Yan mata a Makaranta

  • Iran ta bayyana cewa ta za ta taba manta wa da harin da Amurka ta kai kan dalibanta a ranar farko na yakin da suka jawo ba
  • A wannan mummunan hari da ya tayar da hankulan jama'a fiye da dalibai 16o ne suka rasu bayan Amurka da Isra'ila sun jefa bam
  • Duk da Shugaban Amurka Donlad Trump ya sha musanta zargin sun tafka danyen aiki, bincike ya tabbatar da cewa Amurka ce ta kashe yaran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Jakadan Iran a Moscow, Kazem Jalili, ya bayyana cewa gwamnatin Iran za ta nemi diyya daga Amurka da Isra'ila kan kashe daliban kasar.

A ranar farko da harin da kasashen Yahudun da Nasaran suka kai wa Iran, sun jefa bama-bamai a kan makarantar ‘yan mata a kudancin kasar.

Kara karanta wannan

"Ba mu miƙa wuya ga azzalumai": Iran ta gindaya sharadin kawo ƙarshen yaƙi da Amurka

Iran za ta nemi diyya daga Amurka da Isra'ila
Mojtaba Khamenei, jagoran addini da Iran da rakiyar tawagarsa Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Aljazeera ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a birnin Minab, inda aka samu asarar rayuka masu yawa.

Iran ta shiga kunci kan kashe dalibai

A cewar jami’an Iran, wannan hari ya girgiza al’umma tare da jefa iyalai da dama a cikin jimami, musamman ganin cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne kanana.

Jakadan ya ce matakin neman diyya wani bangare ne na kokarin Iran na tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma iyalansu.

Iran ta ce dole ta bi hakkin mutanenta da Amurka ta kashe
Shugaban kasar Amurka, Donald J Trump Hoto: Donald Trump
Source: Getty Images

Ya kara da cewa gwamnatin kasar ba za ta yi shiru ba kan wannan lamari, domin kuwa hakan ya shafi rayuwar fararen hula ne da ba su yi laifin komai ba.

Bayan aukuwar harin da ya faru a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026 hukumomin Iran sun kaddamar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Sakamakon binciken, a cewar jami’an kasar, ya nuna alamun cewa Amurka na da hannu a kai harin, yayin da wani binciken da aka yi a Amurka ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka

Iran za ta nemi hakkin mutanenta

Kazem Jalili ya jaddada cewa hujjojin da aka tattara sun isa su tabbatar da zargin da ake yi, duk da cewa bai bayyana cikakken bayani ba kan irin wadannan hujjoji.

Sai dai ya ce Iran za ta bi duk hanyoyin shari’a na kasa da kasa domin neman hakkinta da jinin yaranta da aka salwantar.

Wannan batu ya kara dagula dangantaka tsakanin Iran da kasashen Yamma, musamman Amurka da har yanzu ake gwabza yaki da ita.

Har ila yau, Isra’ila, wacce ita ma aka ambace ta a cikin zargin, ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba.

Kasar Iran za ta hukunta Amurka

A baya, kun samu labarin cewa mahukunta a birnin Tehran na ci gaba da jimamin nutsar da jirgin ruwan yakin Iran da Amurka ta yi a cikin teku a yakin da ke gudana.

Babban kwamandan rundunar sojojin ruwan Iran, Rear Admiral Shahram Irani, ya bayyana cewa ana ci gaba da bakin ciki kan kisan da aka yi wa sojojin da ke jirgin.

Ya bayyana cewa kisan da aka yi wa sojojin ruwan ba zai tafi a banza ba domin akwai shirin da suka yi na daukar fansa rayukan jami'an da aka barnatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng