Kasashe 5 da Za Su Iya Shiga cikin Yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Kasashe 5 da Za Su Iya Shiga cikin Yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Birnin Tehran, Iran - Kasashen Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashen da za su iya shiga yakin Amurka, Isra'ila da Iran
Shugaban kasar China, Xi Jin Ping, Shugaba Donald Trump na Amurka da Mojtaba Khamenei Hoto: Clament Thian, Heather Diehl, Reza B
Source: Getty Images

Kasashen da za su iya shiga yakin Iran

Tashar Axios ta tattaro wasu kasashen da za su iya shiga cikin yakin idan ya ci gaba da fadada.

Idan manyan ƙasashe kamar China ko Rasha suka shiga fadan fiye da yadda suke yanzu, rikicin yankin Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazanar faɗaɗa zuwa wani abu mafi muni.

Rikicin na iya zama fafatawa ta kai-tsaye tsakanin Amurka da Rasha ta hanyar wasu, ko kuma matsalar makamashi ta duniya wadda za ta tilasta wa China ɗaukar mataki.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Ga jerin wasu kasashen da za su iya shiga cikin rikicin:

1. China

Tun farko China ta yi Allah-wadai da hare-haren Amurka a matsayin saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.

China ta yi Allah wadai da harin Amurka kan Iran
Shugaban kasar China, Xi Jin Ping Hoto: Vincent Thian
Source: Getty Images

China ta matsa lamba don rage zaman ɗar-ɗar a wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, yayin da ta kwashe fiye da 'yan ƙasarta 3,000 daga Iran.

Ganin yadda take dogaro da mashigar Hormuz wajen shigo da kashi 80 na man fetur ɗinta daga Iran, China tana matsa wa Tehran lamba don samar da hanyar wucewa cikin aminci ta wannan muhimmiyar hanyar ruwa.

Tashar CNN ta ambato Ministan harkokin wajen China yana cewa:

"Wannan yaƙi ne da bai kamata ya faru ba, kuma yaƙi ne da babu wanda ya amfana da shi."

China da Iran na da kyakkyawar alaka ta diflomasiyya kuma akwai alamun da ke nuna cewa China tana taimakon Iran a yakin da ake yi.

2. Rasha

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fito ta yi Allah wadai kan hare-haren Amurka da Isra'ila a kan kasar Iran.

Kara karanta wannan

Manyan Kasashen duniya 2 da ke samun riba duk da yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Rasha ta nuna goyon baya ga Iran a yakin ta da Amurka
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin Hoto: Sergey Fadelchev
Source: Getty Images

Rasha ta kira harin na Amurka a matsayin wani shirin da aka tsara tun da fari kuma harin wuce gona da iri ne da ba a tsokana ba, kan wata ƙasa mai cin gashin kanta kuma mamba a majalisar dinkin duniya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa cewa Rasha tana ba Iran bayanan sirri don kai hari kan dakarun Amurka.

Ana kuma hasashen Rasha za ta haɓaka jigilar man fetur zuwa Indiya da China yayin da hargitsin Hormuz ke janyo tashin farashi, musamman bayan gwamnatin Donald Trump ta ba Indiya damar sayen man Rasha duk da takunkumi.

3. Turkiyya

Turkiyya ta ce ba za ta amince a yi amfani da sararin samaniyarta wajen kai hari kan Iran ba, wani matsayi mai wuyar fahimta ga ƙasar da take ƙawance da Amurka kuma mamba a NATO.

Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren Amurka kan Iran
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Zaman ɗar-ɗar ɗin ya fito fili bayan NATO ta kakkabo aƙalla makaman linzami guda biyu na Iran da ke nufar yankin Turkiyya.

Kara karanta wannan

Iran ta ji wuta, ta shirya mika wuya ga Amurka? Trump ya yi magana

Turkiyya ta yi Allah-wadai da hare-haren Iran kan Azerbaijan, sannan ta tura jiragen yaƙi F-16 guda shida zuwa Arewacin Cyprus don kare tsibirin Bahar Rum daga hare-haren Iran.

Shigar Kurdawa cikin yakin Iran na iya haifar da martani daga Turkiyya, wadda ta daɗe tana adawa da Kurdawan.

4. Yemen

'Yan tawayen Houthi na Yemen da Iran ke marawa baya ba su riga sun shiga yaƙin ba, amma sun nuna alamun cewa za su iya shiga.

Houthi na iya shiga yakin Iran, Amurka da Iara'ola
Magoya bayan Houthi na zanga-zangar kashe Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Mohammed Huwais
Source: Getty Images

Shigar su za ta buɗe wani sabon fagen yaƙi kuma ya yi barazana ga jigilar jiragen ruwa a tekun Red Sea.

Yemen na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka ambata a cikin gargaɗin ma'aikatar harkokin wajen Amurka na cewa Amurkawa su gudu saboda kusancinta da Iran da kuma goyon bayan da Houthis ke ba wa gwamnatin Iran.

5. Ukraine

Kasar Ukraine tuni tana haɗa kai da Amurka da ƙasashen Gulf kan kariya daga jirage marasa matuƙa na Shahed.

Ukraine za ta iya shiga yakin Amurka da Iran
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky Hoto: @ZelenskyUa
Source: Twitter

Ukraine tana amfani da ƙwarewarta da ta samu wajen daƙile jirage marasa matuka na Shahed na Iran a yaƙin Rasha.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a wani rubutu a shafinsa na X, ya ce kasashen Gabas ta Tsakiya sun nemi taimako wajen dakile hare-haren jirage marasa matuka na Iran.

Kara karanta wannan

Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran

Ya bayyana cewa a shirye suke su taimaka, kuma tuni kasarsa ta tura wasu kwararru ta wannan fannin zuwa kasashe uku a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai, Iran ta yi barazanar kai hari kan Ukraine idan ta ba da taimako a yakin da ake yi.

Donald Trump ya gargadi Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aika da sakon gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

​Trump ya gargadi Iran cewa Amurka za ta mayar da martani mai tsauri idan kasar ta dauki wani mataki da zai hana zirga-zirgar mai a mashigar Hormuz.

Shugaban na Amurka ya ce kasarsa ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai kawo cikas ga safarar mai a wannan muhimmin wuri na duniya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng