NATO: Trump Ya Fara Yi wa Turai Mummunan Fata kan Kin Taya Shi Yakar Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya matsawa kasashe lamba game da neman su taimaka masa wajen hada kai su yaki kasar Iran
- Ya nemi kasashen da toshe mashigar Hormuz ya shafa su tura jiragen yaki domin gwabzawa da dakarun Iran da suka hana wucewa ta hanyar
- Biyo bayan alamun rashin samun goyon baya, Trump ya fara sukar kasashen da suka ki amsa kiranshi tare da yin gargadi ga kasashen NATO
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Donald Trump, ya gargadi kasashen kawancen NATO cewa za su fuskanci matsala idan ba su taimaka wa Amurka wajen tabbatar da tsaron mashigar ruwan Hormuz ba.
Yakin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya shiga mako na uku, kuma Trump ya ce yana tattaunawa da kusan kasashe bakwai domin su taimaka wajen kare mashigar ruwan.

Source: Getty Images
Iran: Gargadin Trump ga NATO
A wata hira da ya yi da jaridar Financial Times ta Birtaniya, Trump ya ce karshen kasashen kawancen NATO ba zai yi kyau ba idan ba su taimaka wa Amurka wajen kare muhimmiyar hanyar ruwa ta Hormuz ba.
Trump ya kara da cewa ya kamata kasashen da ke amfana da jigilar man fetur da ke ratsa Tekun Fasha su taimaka wajen kare mashigin ruwan.
Amurka da Isra’ila sun kaddamar da yaki kan Iran a karshen watan da ya gabata, lamarin da ya jawo martani daga Tehran a yankin.
Iran ta dauki matakin rufe mashigar Hormuz a matsayin martani, abin da ya sa farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya tare da kara matsin tattalin arziki kan Trump da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
Martanin kasashen Turai ga Trump
A bangaren Tarayyar Turai kuwa, jami’an kungiyar sun ce kasashen mambobinta za su tattauna kan matakan da za a dauka domin tabbatar da cewa mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a bude.
Babbar jami’ar kula da harkokin waje ta Tarayyar Turai, Kaja Kallas, ta ce bude mashigar Hormuz yana da muhimmanci ga kasashen Turai.
“Yana da muhimmanci a gare mu a tabbatar da cewa mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a bude,”
Inji ta gabanin taron ministocin harkokin wajen kungiyar a birnin Brussels.
Bayanin da China ta yi
A bangaren China kuwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Lin Jian, ya ce tashin hankalin da ake fuskanta ya kawo cikas ga hanyoyin kasuwanci tare da barazana ga zaman lafiya a yankin da duniya baki daya.
BBC ta rahoto ya kara da cewa China na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da ayyukan soja nan take tare da rage tashin hankalin da ake fuskanta.
Faransa ta mikawa Iran bukatu
A wani labarin, kun ji cewa, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi waya da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian.
A tattaunawar da suka yi, Macron ya ce ya bukaci Iran ta bude mashigar Hormuz domin jiragen kasashen katare su samu damar wucewa.
Baya ga haka, ya ce Faransa na bukatar Iran da dakatar da kai hare-hare kasashen yankin Gabas ta Tsakiya kamar Qatar, Saudi da sauransu.
Asali: Legit.ng

