Isra’ila Ta Fadi Matsalar da Ta Ke Fuskanta yayin Yaki da Iran
- Rahoto ya nuna cewa Isra'ila na fuskantar karancin makaman kare kai daga makamai masu linzami yayin yakin da take yi da Iran
- Wani jami’in Amurka ya ce kasarsa ba ta fuskantar irin wannan matsala duk da yakin da take yi tare da Isra'ila
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yakin da ake yi da Iran zai ci gaba muddin har akwai bukatar hakan kuma ba za su sare ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Tel Aviv, Isra'ila - Rahotanni sun bayyana cewa kasar Isra'ila na fuskantar karancin makaman kare kai daga makamai masu linzami.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin kasar da Iran wanda ke neman ruguza tattalin arzikin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
An gano matsalar da Isra'ila ke ciki
Wannan bayani ya fito ne a cikin wani rahoto da kafar labarai ta TRT World ta wallafa, inda ta ambato wani jami’in gwamnati daga Amurka.
A cewar jami’in, gwamnatin Amurka ta dade da sanin cewa Isra'ila na fama da karancin makaman kare kai tun watanni da suka gabata wanda na daga cikin matsalolin da ta ke fuskanta a yanzu.
Sai dai jami’in ya jaddada cewa Amurka ba ta fuskantar irin wannan matsala duk da yakin da take yi tare da Isra’ila.
Ya ce kasarsa na da isassun makamai domin kare sansanonin sojojinta da ma’aikatanta da kuma muradunta a yankin.
Haka kuma ya ce Isra'ila na kokarin nemo hanyoyin magance karancin makaman da take fuskanta, cewar Times of Israel.

Source: Getty Images
Alfaharin da Trump ya yi a farko
Rahoton ya kuma nuna cewa Isra'ila ta fara yakin ne da Iran duk da cewa tun farko tana da karancin wadannan makamai.
A baya dai shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa kasarsa na da makamai da yawa da za ta iya amfani da su a yakin.
A farkon rikicin, Trump ya ce yakin na iya daukar kusan makonni hudu kacal, sai dai daga baya ya ce yakin na iya ci gaba na wani dan lokaci kadan.
A ranar Juma’a 13 ga watan Maris din shekarar 2026 kuma ya sake bayyana cewa yakin da ake yi da Iran zai ci gaba muddin har akwai bukatar hakan.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Rahoton wani binciken bayanan sirri da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito ya nuna cewa gwamnatin Iran ba ta kusa rushewa ba duk da hare-haren da ake kai mata.
Trump ya magantu kan lokacin da yaki zai kare
An ji cewa shugaba Donald Trump, ya yi magana kan lokacin da yakin da ake tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.
Trump ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai yana mai cewa zai gane lokacin da yakin ya kare “idan ya ji a cikin ransa”.
Shugaban na Amurka ya kuma ce dakarun kasarsa na samun gagarumar nasara a yakin da suke yi tare da Isra'ila kan Iran.
Asali: Legit.ng
