Abin da Shugaban Iran Ya Tattauna da Macron, Ya Gindaya Sharaɗin Tsagaita Wuta
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana game da kiran a tsagaita wuta a yakin da kasar ke yi da Isra'ila
- Pezeshkian ya ce tattaunawar tsagaita wuta ba ta da amfani muddin babu tabbacin cewa ba za a sake kai hare-hare ba
- Ya bayyana hakan ne bayan tattaunawa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, inda ya zargi Amurka da Isra'ila da kai hari kan Iran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi karin haske game da kiran a tsagaita wuta a yakin kasar da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.
Pezeshkian ya ce babu ma’ana a tattauna batun tsagaita wuta idan ba a tabbatar da cewa ba za a sake kai wa kasarsa hari ba nan gaba kamar yadda aka yi yanzu.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban ya wallafa a X a jiya Litinin 16 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.
Yadda yaki ya barke tsakanin Iran da Isra'ila
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila da ta ke samun goyon bayan kasar Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.
An fara yakin ne tun a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 wanda Isra'ila da hadin guiwar Amurka suka kai hari a birnin Tehran.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar jagoran addinin Musulunci na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan shugabannin tsaro.
Shugaban Iran ya magantu kan tsagaita wuta
A sakon da ya wallafa, ya yi ishara da tattaunawar wayar da ya yi da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, kan hare-haren da ya danganta da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan
"Ba mu miƙa wuya ga azzalumai": Iran ta gindaya sharadin kawo ƙarshen yaƙi da Amurka
Ya bayyana cewa ba Iran ba ce ta fara wannan mummunan yaki inda ya ce ya halatta kasar ta kare kanta daga mamaya.
Ya ce:
“Iran ba ita ce ta fara wannan mummunan yaki ba, yana mai kara da cewa kare kai daga mamaya hakki ne na halitta wanda kasar ke iya yi sosai."

Source: Facebook
Sharadin shugaban Iran kan yaki da Isra'ila
Shugaban ya jaddada cewa magana kan kawo karshen yaki ba ta da amfani har sai an tabbatar da cewa ba za a sake kai hare-hare a cikin kasar ba nan gaba.
Haka kuma ya bukaci a kawo karshen amfani da sansanonin Amurka a yankin domin kai hare-hare kan Iran, yana cewa hakan na lalata dangantakar Tehran da makwabtanta.
An gano yawan albashin Shugaban Iran
A baya, an ji cewa Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana kan tattalin arziki yayin da ake ci gaba da yakin tsakanin kasar da Isra'ila.
Pezeshkian ya bayyana yawan albashinsa na shugaban kasa a wata ba saboda matsalar kudin kasar inda ya ce bai wuce $1,000 ba kacal.
Ya amince cewa matsin tattalin arziki ya sa mutane da dama sun nuna rashin jin dadi ga gwamnatin Iran wanda ya jawo zanga-zanga a kasar baki daya.
Asali: Legit.ng
