Tirkashi: Donald Trump Ya Yanke Lokacin da Yakin Iran da Isra’ila Zai Kare

Tirkashi: Donald Trump Ya Yanke Lokacin da Yakin Iran da Isra’ila Zai Kare

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan lokacin da yakin da ake tsakanin Iran da Isra'ila
  • Trump ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai yana mai cewa zai gane lokacin da yakin ya kare “idan ya ji a cikin ransa”
  • Shugaban na Amurka ya kuma ce dakarun kasarsa na samun gagarumar nasara a yakin da suke yi tare da Isra'ila kan Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan ci gaba da yaki da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.

Trump ya bayyana cewa yakin da ake yi tsakanin kasarsa da Iran zai zo karshe ne idan ya ji a zuciyarsa cewa lokacin kawo karshensa ya yi.

Trump ya magantu kan kawo karshen yaki da Iran
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump Hoto: Anadolu.
Source: Twitter

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin The Brian Kilmeade Show wanda Brian Kilmeade ke gabatarwa wanda CNN ta bibiya.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Iran/Isra'ila: Trump ya nuna kwarin guiwa

Hirar ta gudana kusan makonni biyu bayan fara hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai kan wurare daban-daban a Iran.

A yayin hirar, Trump ya nuna kwarin gwiwa cewa al’amura za su daidaita cikin sauri bayan an kawo karshen yakin.

Ya ce:

“Idan yakin ya kare, kuma bana ganin zai dauki lokaci mai tsawo ba, abubuwa za su farfado cikin sauri.”
Trump ya sha alwashi kan yaki da Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Trump ya magantu kan karshen yaki da Iran

Mai gabatar da shirin, Brian Kilmeade, ya tambayi shugaban yadda zai san lokacin da ya dace a kawo karshen yakin.

Trump ya amsa da cewa zai gane hakan ne idan ya ji a zuciyarsa cewa lokaci ya yi.

Ya ce:

“Idan na ji hakan, idan na ji a cikin ƙasusuwana.”

Lokacin da aka tambaye shi ko kawo karshen yakin zai kasance shawarar hadin gwiwa, Trump ya yabawa manyan jami’an gwamnatinsa da shugabannin soji.

Daga cikin wadanda ya ambata akwai Dan Caine da ministan tsaro Pete Hegseth, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Trump ya yi fatali da bukatar Putin kan yakin Amurka da Iran

Haka kuma ya ambaci ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio da mataimakin shugaban kasa, JD Vance.

A baya dai shugaban ya bayyana lokuta daban-daban kan tsawon lokacin da yakin zai iya dauka.

Bayan kwana biyu da fara hare-haren farko, ya ce yakin na iya daukar makonni hudu zuwa biyar ko ma fiye da haka.

Sai dai daga baya ya ce dakarun Amurka na samun ci gaba cikin sauri fiye da yadda aka yi hasashe.

An yi zanga-zanga a Isra'ila

An ji cewa an gudanar da wata karamar zanga-zangar ƙin jinin yaƙi a Tel Aviv inda mutane suka yi kira ga Isra'ila ta janye daga harin da ake kai wa Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami kan biranen Isra'ila a matsayin martanin kashe manyan kwamandojin yakinta.

Jami'an tsaro a Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zangar saboda dokar ta-ɓaci da kuma fargabar makaman da Iran ke harbawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.