Bidiyo: Yadda Zanga Zanga Ta Barke a Kasar Isra'ila Tana tsakiyar Yaki da Iran

Bidiyo: Yadda Zanga Zanga Ta Barke a Kasar Isra'ila Tana tsakiyar Yaki da Iran

  • An gudanar da wata karamar zanga-zangar ƙin jinin yaƙi a Tel Aviv inda mutane suka yi kira ga Isra'ila ta janye daga harin da ake kai wa Iran
  • Wannan na zuwa ne yayin da Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami kan biranen Isra'ila a matsayin martanin kashe manyan kwamandojin yakinta
  • Jami'an tsaro a Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zangar saboda dokar ta-ɓaci da kuma fargabar makaman da Iran ke harbawa zai iya fadawa kan su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - A ranar 15 ga Maris, 2026, an gudanar da wata ƙaramar zanga-zangar nuna adawa da yaƙi a birnin Tel Aviv na ƙasar Isra'ila, inda masu zanga-zangar suka soki hannun ƙasarsu a hare-haren da ake kai wa Iran.

Hotunan bidiyo da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa sun nuna mutane suna bayyana damuwarsu kan yadda yaƙin ke ƙara kamari tun bayan fara farmakin haɗaka a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Harin da Iran ta kai Isra'ila ya hallaka ɗan uwan Netanyahu? Bayanai sun fito

Zanga zangar adawa da yaki ta barke a kasar Isra'ila
Masu zanga zanga sun mamaye tituna a Tel Aviv (hagu) da Firayin Minista Benjamin Netanyahu (dama). Hoto: Amir Levy/Yair Palti/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Zanga zangar adawa da yaki ta barke a Isra'ila

Masu zanga-zangar sun nuna fargaba kan asarar rayukan mutane da kuma haɗarin da yaƙin zai iya haifar wa daukacin yankin Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda Aljazeera ta rahoto.

Wannan zanga-zangar tana zuwa ne a daidai lokacin da Iran ta harba jerin makaman linzami da jirage marasa matuƙa kan biranen Isra'ila, ciki har da Tel Aviv, a matsayin martani ga kashe tsohon jagoran ƙasar Ali Khamenei.

Hare-haren na Iran sun haifar da lalacewar motoci da gine-gine a tsakiyar Isra'ila, sannan ƙasashen biyu sun tabbatar da samun asarar rayukan farar hula sakamakon luguden wuta da ake yi.

Kalli bidiyon zanga zangar a nan kasa:

Sojojin Isra'ila sun dage da kai hari Iran

Duk da wannan barazana, dakarun Isra'ila (IDF) sun ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro da kuma cibiyoyin bincike na Iran, in ji rahoton Daily Times.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka: Sojojin Isra'ila sun kashe babban malamin addinin Kirista

A ranar 14 ga Maris, rundunar IDF ta sanar da kakkabe manyan jami'an leken asiri guda biyu na Iran daga cibiyar "Khatam al-Anbiya", sannan ta jefa bama-bamai kan wata masana'antar kera makaman kariya da kuma babbar cibiyar binciken sararin samaniya ta Iran.

Wadannan matakai na Isra'ila sun harzuka ƙasar Iran wajen iƙirarin cewa an lalata mata muhimman ababen more rayuwa na jama'a.

Zanga Zanga ta barke a Isra'ila kan yakin da kasar ke yi da Iran.
Masu zanga zanga sun mamaye manyan titunan birnin Tel Aviv na kasar Isra'ila. Hoto: AHMAD GHARABLI / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Karuwar zanga zanga a sassan kasar Isra'ila

Tun farkon yaƙin, ana samun ɓullar zanga-zangar ƙin jinin yaƙi lokaci-lokaci a wurare kamar dandalin Habima dake Tel Aviv, inda mutane ke kiran a tsayar da farmakin soji.

Sai dai akasari jami'an tsaro suna tarwatsa waɗannan taron cikin gaggawa saboda dalilai na tsaron gida, dokar ta-ɓaci kan taron jama'a, ko kuma saboda samun tirjiya daga wasu 'yan ƙasar dake goyon bayan yaƙin a matsayin hanyar kariya.

Wannan zanga-zangar ta ranar 15 ga Maris tana nuna cewa ko da yake yawancin jama'ar Isra'ila suna goyon bayan matakan soja don kariya, akwai wasu dake kalubalantar hakan da ganin illolin da yakin ke haifarwa duniya baki ɗaya.

Iran ta kaddamar da hari mafi muni

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojojin Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta ƙaddamar da rukuni na 37 na farmakin nan mai suna “True Promise 4”.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

Rundunar juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran ta bayyana sabon rukunin na 37 a matsayin hari mafi muni da aka taɓa kaiwa tun farkon fara yakin.

Dakarun sun ce samamen ya haɗa da hare-hare kan wurare a Tel Aviv da sauran wurare a cikin Isra'ila, tare da sansanonin da ke da alaƙa da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com