Mashigar Hormuz: Kasashe 5 Sun Kunyata Donald Trump bayan Bukatarsa Gare Su

Mashigar Hormuz: Kasashe 5 Sun Kunyata Donald Trump bayan Bukatarsa Gare Su

  • Donald Trump ya bukaci kasashe biyar su tura jiragen yaki zuwa mashigar Hormuz amma har yanzu babu wanda ya amince
  • Japan da Faransa sun nuna rashin amincewa da bukatar, yayin da Birtaniya ke tattaunawa da kawaye
  • Ana fargabar Iran ta dasa nakiyoyi a mashigin ruwan da ke da muhimmanci ga safarar man fetur ta duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bukaci wasu manyan kasashe su tura jiragen yaki zuwa mashigar Hormuz domin rakiyar jiragen dakon mai.

Wannan mataki na zuwa ne bayan Iran ta rufe mashigin ruwan, lamarin da ya kawo cikas ga safarar makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashe sun kunyata Trump kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Sai dai har zuwa yanzu babu wata kasa daga cikin wadannan da ta amince da bukatar, cewar rahoton RFI Hausa.

Kara karanta wannan

Tofa: Iran ta gagari Trump, ya fara neman dauki wajen manyan kasashen duniya

Bukatar Trump ga kasashe 5 kan mashigar Hormuz

Trump ya bukaci kasashen China da Faransa da Japan da Korea ta Kudu da kuma Birtaniya su tura jiragen yakinsu domin kalubalantar shingen da Iran ta kafa.

Japan ce kasa ta farko da ta mayar da martani, inda ta bayyana cewa ba za ta aika jiragen yaki zuwa mashigin ba kawai saboda bukatar Trump.

A nata bangaren, Birtaniya ta ce tana tattaunawa da kawayenta domin nemo hanyoyin dawo da zirga-zirgar makamashi a yankin.

China kuwa ta jaddada cewa tana son bangarorin da ke rikici su dakatar da fada domin dawo da zaman lafiya da kuma kasuwancin makamashi.

Kasashe sun yi biris da bukatar Trump kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump na Amurka da mashigar Hormuz. Hoto: FADEL SENNA.
Source: Getty Images

Abin da Faransa ta ce kan bukatar Trump

Haka kuma France ta bayyana cewa ba za ta tura jiragen yakinta zuwa mashigar ruwa Hormuz ba.

Ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa babu wani jirgin yaki na Faransa da za a tura zuwa yankin Tekun Mediterranean saboda wannan rikici.

Sai dai shugaban South Korea ya ce kasarsa na nazarin bukatar da Trump ya gabatar, tare da tattaunawa da Amurka kan lamarin, cewar Globe Eye News.

Kara karanta wannan

Rasha: Amurka ta fara bakin jini a Turai saboda yakin Iran

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu hukumomin tsaro na Amurka sun nuna damuwa kan hadarin tura jiragen yaki domin kare jiragen dakon mai a mashigin.

Ana kuma fargabar cewa Iran na iya dasa nakiyoyi a cikin mashigar Hormuz, lamarin da zai iya kara tsananta rikicin yankin.

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu hukumomin tsaro na Amurka sun nuna damuwa kan hadarin tura jiragen yaki domin kare jiragen dakon mai a mashigin.

Ana kuma fargabar cewa Iran na iya dasa nakiyoyi a cikin mashigar ruwa ta Hormuz, lamarin da zai iya kara tsananta rikicin yankin.

Isra'ila: Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta

A wani labarin, babban sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani, ya kalubalanci Shugaba Donald Trump kan bugun kirji game da yakin da ake yi.

Ali Larijani ya ce Iran ba za ta daina yaki ba sai Amurka ta yi nadamar fara yakin da ta yi ita da Isra'ila da wasu makiya.

Rikicin Iran, Isra'ila da Amurka ya girgiza kasuwar makamashi tare da dakile zirga-zirga a mashigar Hormuz wanda ya ke taba tattalin arzikin kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.