Abin da Iran Ta Ce kan Ganin bayan Netanyahu yayin da Ake Rade Radin Ya Mutu
- Rundunar IRGC ta Iran ta yi barazanar kashe Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu
- Barazanar ta zo ne bayan harin hadin gwiwa na Isra'ila da Amurka da ya kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei
- Rikicin ya kara tsananta bayan harin makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki da bangarorin biyu ke ci gaba da kai wa juna
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Rundunar juyin juya hali ta Iran watau 'Islamic Revolutionary Guard Corps' ta yi magana kan Benjamin Netanyahu.
Rundunar ta yi barazanar kashe Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu domin daukar fansa kan hare-haren da ya kai mata.

Source: Getty Images
Rundunar IRGC ta kada hantar Netanyahu
A wata sanarwa da aka wallafa a shafinta wanda Al-Awsat ta gano, rundunar ta ce za ta ci gaba da farautar Netanyahu har sai ta kashe shi.

Kara karanta wannan
Isra'la ta kashe babban kwamandan Iran, an jero kwamandojoji 3 da suka mutu a baya
Sanarwar ta ce:
“Idan wannan mai aikata laifin kashe yara yana raye, za mu ci gaba da binsa har sai mun kashe shi da dukkan karfinmu.”
Barazanar ta zo ne bayan jita-jitar da ta bazu a kafafen sada zumunta cewa an kashe Netanyahu.
Sai dai rundunar tsaron Isra'ila ta karyata jita-jitar, inda hukumomin Isra'ila suka ce labarin ba gaskiya ba ne.
Rikicin ya kara tsananta ne bayan harin sama da Isra'ila da Amurka suka kai kan wurare da dama a Iran a ranar 28 ga Fabrairu 2026.
Harin ya yi sanadin mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, da wasu manyan jami’an gwamnati da dama.
Bayan haka, Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan Isra'ila da kuma sansanonin sojojin Amurka a yankin.

Source: Getty Images
Wadanda suka jikkata a Isra'ila
Haka kuma, ma’aikatar lafiya ta Isra'ila ta ce mutane 108 da suka jikkata sakamakon rikicin an kai su asibitoci cikin awanni 24 da suka gabata.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Ma’aikatar ta ce biyu daga cikinsu suna cikin matsakaicin hali, yayin da mafi yawansu ke cikin yanayi mai sauki.
Tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairu, mutane 3,195 ne aka kai asibiti saboda raunukan da suka samu, cewar France 24.
Daga cikinsu, mutum daya na cikin mawuyacin hali, yayin da wasu tara ke cikin mummunan yanayi.
A daya bangaren kuma, shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran na son kulla yarjejeniya da Amurka.
Sai dai ya ce har yanzu bai shirya amincewa da yarjejeniyar ba saboda sharuddan ba su gamsar da shi ba.
Trump ya kuma ce ba a tabbatar ba ko sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei yana raye, tare da bayyana rashin tabbas kan ko Iran ta jefa nakiyoyi a mashigin ruwa na ta Hormuz.
Iran ta harba makamai masu linzami a UAE
An ji cewa kasar Iran ta harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan lamarin ya jikkata mutane sama da 140 ciki har da ‘yan Najeriya wanda ya tayar da hankali matuka.
Harin ya tayar da hankalin dubban ‘yan Najeriya mazauna UAE, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta.
Asali: Legit.ng