Babbar Magana: Trump Ya Yi Fatali da Bukatar Putin kan Yakin Amurka da Iran

Babbar Magana: Trump Ya Yi Fatali da Bukatar Putin kan Yakin Amurka da Iran

  • Shugaban kasar Iran, Vladimir Putin, ya yi yunkurin shiga tsakani domin ganin an kawo karshen yakin Amurka, Isra'ila da Iran
  • A yayin wata tattaunawa da ya yi da Donald Trump, Putin ya ba da shawarar hanyar da za a iya samun zaman lafiya
  • Sai dai, Donald Trump, ya kafa ya yi fatali da shawarar da Trump ya ba da wacce ko a baya ya taba ba da irinta

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wata tattaunawa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin.

A yayin tattaunawar ta wayar tarho da suka yi, Shugaba Vladimir Putin ya ba da shawarar kwashe sinadarin uranium na Iran da aka inganta zuwa ƙasar Rasha a matsayin ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

Putin ya shiga tsakani a yakin Rasha da Amurka
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin da Shugaba Vladimir Putin na Rasha Hoto: Sergei Fadelchev, Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Tashar Axios ta kawo rahoton cewa majiyoyi sun gaya mata cewa Trump ya ƙi amincewa da tayin na Putin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema

Ana takaddama kan Uranium din Iran

Tabbatar da tsaron kilo 450 na sinadarin uranium na Iran da aka inganta zuwa 60%, wanda za a iya mayar da shi matakin kera makaman yaki a cikin 'yan makonni, kuma ya isa kera bama-baman nukiliya sama da 10, yana ɗaya daga cikin manyan manufofin yaƙi na Amurka da Isra'ila.

A ka'idance, tayin na Putin zai iya taimaka wa wajen kwashe rumbun nukiliyar Iran ba tare da bukatar dakarun Amurka ko na Isra'ila sun shiga cikin ƙasar ba.

Rasha dama riga ta kasance ƙasa mai ƙarfin nukiliya, kuma a baya ta taɓa ajiye sinadarin uranium na Iran da aka inganta shi kaɗan a ƙarƙashin yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

Hakan ya sa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe kaɗan da ke da ƙarfin fasaha na karɓar irin wannan sinadari.

Vladimir Putin ya ba Donald Trump shawara

Putin ya gabatar da ra'ayoyi da dama na kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Amurka da Iran a wayar da suka yi da Trump ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Trump ya gano shugaban kasa 1 da zai iya taimakon Iran a yaki da Amurka, Isra'ila

Shawarar kwashe uranium ɗin tana ɗaya daga cikinsu.

Wani jami'in Amurka ya bayyana cewa:

"Wannan ba shi ne karon farko da aka ba da wannan shawarar ba. Ba a amince da ita ba. Matsayin Amurka shi ne muna buƙatar ganin an tabbatar da tsaron uranium ɗin."
Trump ya ki amincewa da shawarar Putin
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Rasha ta sha shiga tsakanin Amurka, Iran

Rasha ta taɓa gabatar da makamanciyar wannan shawarar lokacin tattaunawar nukiliya tsakanin Amurka da Iran a watan Mayun 2025, kafin Amurka da Isra'ila su kai hari kan wuraren nukiliyar Iran a watan Yuni da kuma makonni kafin fara yaƙin na yanzu.

A zagayen ƙarshe na tattaunawa kafin yaƙin, Iran ta yi watsi da ra'ayin mayar da sinadarin zuwa wata ƙasar, inda ta ba da shawarar rage ƙarfin sinadarin uranium ɗin a cikin nata wuraren ayyukan ƙarƙashin kulawar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA).

Ba a bayyana cewa ko a yanzu Iran za ta amince da shawarar ba.

Kasar Iran ta gargadi Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta aika da sakon gargadi ga Amurka kan kada ta yi yunkurin kashe Mojtaba Khamenei.

Kara karanta wannan

Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran

Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya yi gargadin cewa Amurka za ta fuskanci martani mai tsanani idan ta yi ƙoƙarin kashe sabon jagoran addini na Iran.

Ya bayyana cewa jama'a suna cikin fushi da tsananin bukatar ganin an dauki fansar kisan da aka yi wa Ayatollah Ali Khamenei.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng