Trump Ya Harba Bama Bamai Iran, Ya Ce Amurka Ta kai Hari Mafi Muni a Tarihi

Trump Ya Harba Bama Bamai Iran, Ya Ce Amurka Ta kai Hari Mafi Muni a Tarihi

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa ya kai mummunan hari tsibirin Kharg da ke kasar Iran bayan barazanar da ya yi
  • Tsibirin Kharg daya ne daga cikin muhimman wuraren da Iran ke hako danyen mai da ke zama kashin habaka tattalin arzikinta a yau
  • Gwamnatin Iran ta fitar da gargadi game da ikirarin da shugaba Trump ya yi, ta ce za ta yi martani mai zafi a kan duk wani hari da aka kai mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Yakin da ake a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila na cigaba da daukar zafi bayan Donald Trump ya sanar da kai hari tsibirin Kharg.

Hakan na zuwa ne bayan shiga mako na biyu da fara yakin da Amurka/Isra'ila suka kaddamar a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da za su hana Donald Trump iya cewa ya yi nasara kan Iran

Ayatollah Ali Khamenei da Donald Trump
Marigayi Ayatollah Ali Khamenei da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Donald Trump ya ce zai cigaba da kai hari tsibirin Kharg matukar Iran ta cigaba da toshe mashigar Hormuz.

Donald Trump ya kai mummunan hari Iran

Donald Trump ya ce ya aiwatar da daya daga cikin manyan hare-haren bama-bamai mafi karfi a tarihin Gabas ta Tsakiya, inda ta lalata gaba dayan wuraren soja da ke tsibirin Kharg na Iran.

Ya ce:

“Na zabi kada in lalata cibiyoyin man fetur da ke tsibirin. Amma idan Iran, ko wani, ya yi wani abu da zai hana zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, zan sake duba wannan matakin nan take.”

Trump ya kuma bukaci Iran ta ajiye makamanta, tana mai cewa idan ta yi haka za ta tsira da sauran abin da ya rage bai lalata ba a kasar.

Muhimmancin tsibirin Kharg ga Iran

Rahoton BBC ya nuna cewa Kharg tsibiri ne mai tsawon kusan mil biyar, wanda ke da tazarar kusan mil 15 daga gabar tekun Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta

An ce duk da ba mutane da yawa ke zaune a tsibirin ba, kusan kashi 90 cikin 100 na danyen man fetur da Iran ke fitarwa zuwa kasashen waje yana ratsawa ta wurin.

Manyan jiragen daukar mai kan kawo man fetur zuwa tsibirin, daga nan kuma a tura shi ta Tekun Persian da mashigar Hormuz zuwa kasashe daban-daban, musamman China wadda ita ce babbar mai sayen man Iran.

Wasu jirage da suka nufi mashigar Hormuz
Yadda wani jirgin ruwa ya nufi mashigar Hormuz a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa idan aka hana zirga-zirga zuwa tsibirin, hakan zai yi matukar illa ga tattalin arzikin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kasar Iran ta yi gargadi ga Amurka

Iran ta ce kai hari kan cibiyoyinta na man fetur da makamashi zai haifar da kai hari kan cibiyoyin makamashi na kamfanonin mai da ke hada kai da Amurka a yankin.

Wannan gargadin daga rundunar sojin Iran ya biyo bayan sanarwar da Donald Trump ya yi cewa sojojin Amurka sun lalata gaba dayan wuraren soja da ke tsibirin Kharg.

Amurka: Ana kokarin shawo kan Iran

A wani labarin, kun ji cewa Amurka na amfani da wasu kasashe domin shawo kan Iran ta zauna a teburin sulhu a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Gazawar Isra'ila ta fito, Netanyahu ya fara korafi kan rashin kudi

An bayyana cewa kasashen da ke magana da Iran sun hada da Pakistan, Turkiyya da sauransu amma kuma har yanzu ba a cimma matsaya ba.

Shugabannin Iran sun fitar da sharudan tsagaita wuta ko ma yin sulhu, ciki har da neman biyan diyya da yarjejeniyar daina kai mata hari a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng