Babbar Magana: Iran Ta Shirya Yi Wa Amurka da Isra'ila Abin da ba Za Su Taba Mantawa ba
- Gwamnatin Iran ta jaddada cewa sojojin kasar a shirye suke su cu gaba da gwabzawa da kasashen Amurka da Isra'ila
- A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta ce sun shirya koya wa Amurka da Isra'ila darasin da ba su taba gani ba
- Ta ce Iran na son nuna wa abokan gabanta cewa ba zai yiwu su fara yaki sannan su nemi tsagaita wuta a lokacin da suka ga dama ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin kasar Iran ta sake jaddada shirinta na ci gaba da mayar da martani kan sansanonin sojojin Amurka da kasar Isra'ila.
Wannan na zuwa ne yayin da yakin da ya barke tsakanin kasashen uku ya shiga rana ta 14 a yau Juma'a, 13 ga watan Maris, 2026.

Source: Twitter
A wani rahoto da NBC News ta ruwaito, gwamnatin Iran ta sha alwashin koya wa Amurka da Isra'ila darasin da ba za su taba mantawa da shi ba.
Iran ta shirya koyawa Amurka darasi
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ce ta bayyana hakan, tana mai cewa dakarun sojojin kasar ta Musulumci sun shirya tunkarar kowane irin kalubale a wannan yaki da ke gudana.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya bayyana cewa sojojin kasar sun kuduri aniyar ci gaba da kai hare-hare domin mayar da martani ga Amurka da kuma Isra'ila a yakin da ke gudana.
A wata hira da ya yi, Baqaei ya ce Iran na son nuna wa abokan gabanta cewa ba za su iya fara yaki sannan su nemi tsagaita wuta a lokacin da suke so ba.
Ya ce:
“Abin da ya fi muhimmanci gare mu shi ne mu nuna wa makiya cewa ba za su fara yaki duk lokacin da suka ga dama ba sannan su kira tsagaita wuta idan suka ga dama.
"Sojojinmu sun kuduri aniyar koya wa makiya darasi mai tsauri da ba za su manta da shi ba.”
Iran ta sake caccakar Shugaba Trump
A gefe guda kuma, shugaban majalisar koli kan harkokin tsaron Iran, Ali Larijani, ya soki shugaban Amurka Donald Trump, yana mai cewa neman nasara cikin gaggawa a yaki ba abu ne mai sauki ba, cewar rahoton Al-Jazeera.
A wani sako da ya fitar, Larijani ya ce:
“Trump yana ganin zai iya samun nasara cikin gaggawa.Abin da ya gaza fahimta shi ne fara yaki abu ne mai sauki, sai dai ba za a iya cin nasara da wasu rubuce-rubuce kaɗan ba.”

Source: Getty Images
Ya kara da cewa Iran ba za ta daina mayar da martani ba har sai ta sanya Amurka ta yi nadamar abin da ya kira babban kuskure.
Larijani ya kammala sakon nasa da alamar #TrumpMustPay, yana nuna cewa Iran na ganin Amurka za ta biya farashin yakin da ta fara.
Iran ta kakkabo jiragen Amurka da Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin kasar Iran sun yi ikirarin cewa sun kakkabo jirage marasa matuki 111 daga ranar da aka fara yaki da Amurka/Isra'ila zuwa yau.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu
Daga daga cikin jiragen yakin Amurka da sojojin Iran suka kakkabo shi ne MQ-9 Reaper, wanda bayanai suka nuna yana da tsada.
Sai dai hukumomin Iran ba su bayyana cikakken bayani ba kan irin nau’ikan jiragen yakin da suka ce sun kakkabo, ko kuma nawa ne daga cikinsu na Amurka ko na Isra’ila.
Asali: Legit.ng

