Trump Ya Gano Shugaban Kasa 1 da Zai Iya Taimakon Iran a Yaki da Amurka, Isra'ila

Trump Ya Gano Shugaban Kasa 1 da Zai Iya Taimakon Iran a Yaki da Amurka, Isra'ila

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce da yiwuwar takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin na taimaka wa Iran a yakin da suke yi
  • Donald Trump ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi ranar Juma'a yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila
  • Ministan tsaron Amurka ya bayyana cewa sojojin kasar da na Isra'ila sun kai hare-hare 15,000 kan Iran daga farkon yakin zuwa yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana zargin shugaban Rasha, Vladimir Putin, na taimaka wa Iran a yakin da take yi da Amurka da Isra'ila.

Trump ya yi wannan furuci ne yayin da wasu majiyoyi suka yi ikirarin Rasha na taimaka wa Jamhuryar Musulunci da bayanan wuraren da sansanin sojin Amurka suke, lamarin da kasar ta musanta.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu

Trump da Putin.
Shugaban Amurka, Donald Trump na takwaransa na Rasha, Vladimir Putin Hoto: Anadolu, Alexender Ziona
Source: Getty Images

A wata hira da ya yi da tashar Fox News, Trump ya ce yana ganin Putin na iya taimaka wa Iran a wannan yaki da ke kara zafi a Gabas ta Tsakiya.

“Ina ganin watakila yana taimaka musu kadan. Kuma shi ma zai iya tunanin cewa mu na taimaka wa Ukraine,” in ji Trump.

Taimakon da ake zargin Rasha na ba Iran

A kwanakin baya an ruwaito cewa kasar Rasha ta bai wa Iran bayanan da ke taimakawa wajen kai hare-hare kan sojojin Amurka a yayin wannan rikici.

A wani bangare kuma, Ministan Tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce sojojin kasar da na Isra’ila sun kai hare-hare sama da 15,000 kan wuraren sojin Iran tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairu.

Hare-haren da Amurka ke kai wa Iran

A cewarsa

"Mun kai hare-hare sama da 1,000 a kowace rana, kuma mun yi nasarar lalata makamai da cibiyoyin sojoji na Iran."

Kara karanta wannan

Birtaniya ta fasa ƙwai, ta faɗi ƙasar da ke taimakawa Iran a yaƙi da Amurka

Ministan ya kuma yi ikirarin cewa hare-haren da suka tsara kai wa a ranar Juma’a, 13 ga watan Maris, 2026 na iya zama mafi muni tun bayan fara yakin.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a wurin taro Hoto: @DonaldJTrump
Source: Getty Images

Hegseth ya ce farmakin da aka kai sun rage karfin kasar Iran wajen mayar da martani, inda ya ce sun lalata cibiyoyin harba makamai masu linzami a kasar ta Musulunci.

Shugaba Trump ya sha yin ikirarin cewa Amurka da Isra'ila sun ci karfin Iran ta hanyar lalata muhimman wurare da kayayyakin sojojin kasar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

An kashe mutane 1,444 a kasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa hukumomin Lafiya a Iran sun fitar da alkaluman mutanen da hare-haren Amurka suka shafa tun daga ranar Asabar, 28 ga Fabrarairu, 2026 zuwa yau.

Ma'aikatar lafiya ta Iran ta bayyana cewa akalla mutane 1,444 sun mutu yayin da 18,551 suka jikkata sakamakon hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa kasar.

Baya ga asarar rayuka, hare-haren sun kuma haddasa lalacewar asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama, rushewar gine-gine da muhimman ababen more rayuwa a Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262