Dalilai 4 da za Su Hana Donald Trump Iya Cewa Ya Yi Nasara kan Iran

Dalilai 4 da za Su Hana Donald Trump Iya Cewa Ya Yi Nasara kan Iran

Duk da yadda Shugaba Donald Trump ke ikirarin ya yi nasara a Iran, an gabatar da wasu dalilai da ke nuna har yanzu da sauran aiki a gabansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Tun farkon makon da ya wuce shugaban Amurka, Donald Trump ke bayyana cewa ya samu nasara a yakin da ya kaddamar a Iran tare da Isra'ila.

Masu sharhi sun bayyana cewa har yanzu babu alamun cewa Donald Trump da gwamnatinsa ta Amurka sun yi nasarar da zai iya bugan kirji ya ce ya gama da Iran.

Shugaba Donald Trump a Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump ya kama kansa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku wani bincike da tashar CNN ta yi, inda ta gabatar da dalilan da ke nuna har yanzu akwai aiki a gaban Trump

Kara karanta wannan

Trump ya harba bama bamai Iran, ya ce Amurka ta kai hari mafi muni a tarihi

1. Rikicin mashigar Hormuz

Takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz da Iran ta yi tare da hare-haren da ake kai wa tankokin mai a Tekun Gulf sun sa farashin mai da na fetur a gidajen mai suka yi tashin gwauron zabi.

Rundunar ruwan Amurka na nuna taka-tsantsan wajen shiga wannan mashigar saboda barazanar makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marasa matuka na sama da na ruwa da Iran ke da su.

Ana ganin babu wata mafita ta soja da za ta iya bude wannan mashiga cikin gaggawa. Ko da kuwa an samu damar wucewa, za a bukaci rakiyar jiragen ruwa akai-akai, abin da ka iya zama nauyi ga rundunonin ruwan Amurka.

Masana na ganin cewa ba yadda Trump zai gamsar da duniya cewa ya yi nasara ba tare da nuna karfi ya bude mashigar Hormuz ba.

2. Batun jagoran addinin Iran

Kashe Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren farko na yakin Amurka da Isra’ila ya sa rikicin ya zama kamar wani yunkurin kai tsaye na sauya gwamnati.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An bankado yadda Amurka ta jefa bam a kan daliban Iran

Saboda haka maye gurbinsa da dansa Mojtaba ya sanya shakku a kan labarin nasarar da Trump ke kokarin gabatarwa. Wannan ya bai wa ‘yan Democrat damar cewa yakin bai yi nasarar da ake nema ba.

Sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei da ya gaji mahaifinsa a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

3. Zaman gwamnatin Iran daram

Trump ya fara yakin da kira ga ‘yan Iran cewa “lokacin ‘yancinku ya zo,” yana mai cewa suna da dama ta musamman su tashi su kifar da gwamnatin da ke mulki.

Amma zuwa yanzu babu wata alama a fili ta bore. Masana da dama na ganin abin da zai fi yiwuwa shi ne gwamnati ta sake murkushe duk wani yunkurin adawa bayan hare-haren Amurka da Isra’ila sun tsaya.

Ko da Trump zai iya ikirarin nasara idan aka rage barazanar Iran ga Gabas ta Tsakiya, hakan ba zai kai matsayin ba masu bore damar karbar mulki ba, wanda aka ce hakan alamar rashin nasara ce.

4. Halin siyasar cikin gida a Amurka

Jami’an gwamnati na kokarin tabbatar wa Amurkawa cewa karin farashin mai da yakin ya haifar na wucin gadi ne kuma wani dan radadi ne na gajeren lokaci.

Yayin da Amurkawa ke makokin sojojin da suka mutu kuma suke kara shan wahalar rayuwa sakamakon tashin farashin fetur da sauran kayayyaki, ba lallai su yi maraba da ikirarin nasarar Trump ba.

Kara karanta wannan

Trump ya yi barazanar kai wa Iran harin da 'ba a taba ganin irin sa ba'

Wasu rahotanni sun nuna maimakon a canza gwamnati a Tehran, fadarWashington na cikin matsala.

Kasar Iran ta jikkata 'yan Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa bayan shafe kwana 14 ana gwabza yaki tsakanin Iran da Isra'ila/Amurka, an kashe daruruwan mutane.

Ma'aikatar lafiyar kasar Isra'ila ta sanar da cewa sama da mutane 2,000 ne suka jikkata a hare-haren da Iran ta shafe kwanaki tana kai mata.

Yayin da ake cigaba da kai hare-hare a kasashen Gabas ta Tsakiya, gwamnatin Iran ta tattauna da India, inda Tehran ta bukaci a yi Allah wadai da harin Isra'ila da Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng