Da Gaske Netanyahu Ya Bata yayin Yakin Isra’ila da Iran? An Samu Bayanai

Da Gaske Netanyahu Ya Bata yayin Yakin Isra’ila da Iran? An Samu Bayanai

  • An yi ta yada wasu rahotanni da suka bazu a kafofin sadarwa cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bace
  • Majiyoyin suka ce wai Netanyahu ya bace na tsawon kwanaki biyar yayin da ake ci da yaki tsakanin Iran da Isra'ila
  • Jita-jitar ta bazu ne a lokacin rikicin kasashen Iran, Isra’ila da Amurka wanda ya haddasa yaduwar bayanan karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Iran - An yada wani sako a shafukan sadarwa da ke ikirarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bace.

Majiyoyin suka ce Netanyahu ya bace ne daga kasar na tsawon kwanaki biyar kuma ba a san inda yake ba.

An karyata rahoton cewa Netanyahu ya bace
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Sai dai binciken da Legit.ng ta gudanar ya nuna cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne kuma labari ne da ke yaudarar mutane.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta

Wani mai amfani da Facebook da ya bayyana kansa a matsayin Norman Finkelstein ne ya wallafa hoton Netanyahu tare da cewa an nemi kama shi amma ya bace daga Isra’ila.

Rahoton da aka yada kan zargin batan Netanyahu

Sakon wanda aka wallafa ranar 11 ga Maris, 2026 ya yi saurin bazuwa a kafafen sada zumunta.

Zu zuwa safiyar ranar 13 ga Maris, 2026, sakon ya samu daruruwan mutane da suka yi ta bibiyarsa, suka yi sharhi da kuma yada shi.

Sai dai binciken da aka yi ta hanyar kayan aikin tantance gaskiya ya nuna cewa ikirarin ba daidai ba ne.

Rahotanni da sababbin hotuna sun tabbatar da cewa Benjamin Netanyahu yana nan a Tel Aviv kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukan ofishinsa.

Ana ta yada jita-jita cewa Netanyahu ya bata a Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila da ke yaki da Iran. Hoto: @netanyahu.
Source: Facebook

An samu sanarwar gwamnati kan 'batan' Netanyahu?

Har ila yau, babu wata sanarwa daga gwamnatin Isra’ila da ke nuna cewa firaministan ya bace ko kuma ba a san inda yake ba.

Babu kuma wata kafar labarai mai sahihanci da ta tabbatar da cewa Netanyahu ya bar kasar ko kuma ya ɓace.

Shaidu da dama sun nuna cewa yana ci gaba da halartar ayyukan gwamnati duk da jita-jitar da ke yawo a intanet.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Gazawar Isra'ila ta fito, Netanyahu ya fara korafi kan rashin kudi

Jita-jitar ta bazu ne a lokacin tashin hankali da ake fama da shi sakamakon yakin da ya hada Iran, Isra’ila da Amurka.

A irin wannan lokaci, bayanan karya da jita-jita kan yadu cikin sauri a kafafen sada zumunta suna haddasa rudani da rashin fahimta.

Saboda haka, ikirarin cewa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bace na kwanaki biyar ba gaskiya ba ne.

Sababbin bayanai da hotuna sun tabbatar da cewa yana nan a Tel Aviv kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na gwamnati.

Netanyahu ya soki sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Kun yi cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ba zai iya fitowa bainar jama’a ba.

Netanyahu ya ce Amurka da Isra'ila na “murkushe” gwamnatin Iran da kungiyar Hezbollah da aka fa tun a farkon shekarun 1980s.

Mojtaba Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da kai hari kan sansanonin sojojin kasar Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.