Iran Ta Fadi Sharadin Tsagaita Wuta kan Amurka, Isra’ila bayan Kuskuren Farmakinta
- Babban sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani, ya kalubalanci Shugaba Donald Trump kan bugun kirji game da yakin da ake yi
- Ali Larijani ya ce Iran ba za ta daina yaki ba sai Amurka ta yi nadamar fara yakin da ta yi ita da Isra'ila da wasu makiya
- Rikicin Iran, Isra'ila da Amurka ya girgiza kasuwar makamashi tare da dakile zirga-zirga a mashigar Hormuz
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Babban sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani, ya yi karin haske kan batun tsagaita wuta a yakin da ake yi.
Larijani ya bayyana cewa kasarsa ba za ta janye daga yaki ba har sai Amurka ta yi nadamar abin da ya kira babban kuskuren da ta yi na fara yaki.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X (Twitter) aranar Alhamis 12 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.
Martanin Larijani ga Trump a yakin Iran/Isra'ila
Larijani ya yi martani ga kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump wanda ya ke bugun kirji game da nasarar da ya ce suna samu kan Iran.
Ya bayyana hakan ne a matsayin martani, yana mai jaddada cewa Iran za ta ci gaba da gwagwarmaya har sai Amurka ta gane kuskuren matakin da ta dauka.
Ya ce Trump na cewa yana neman samun nasara cikin gaggawa a yakin da aka fara da Iran.
Sai dai Larijani ya yi gargadin cewa fara yaki abu ne mai sauki, amma ba za a iya cin nasararsa da wasu ‘yan sakonni a shafukan sada zumunta ba.
Ya ce:
“Trump ya ce yana neman nasara cikin gaggawa. Amma fara yaki abu ne mai sauki, kuma ba za a iya cin sa da wasu sakonni a X ba.”

Source: Getty Images
Iran ta ja layi kan yaki da Amurka
Larijani ya kara da cewa Iran ba za ta daina kai hari ba har sai Amurka ta yi nadamar abin da ya kira babban kuskuren da ta aikata.
A halin yanzu, yakin da Amurka da Isra'ila suka fara kan Iran ya bazu a yankin Tekun Fasha da wasu wurare.
Rikicin ya haifar da matsaloli a kasuwannin makamashi na duniya tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci.
Haka kuma zirga-zirgar jiragen ruwa ta kusa tsayawa a mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanya da kaso mai yawa na man fetur na duniya ke bi ta cikinta.
Sakamakon haka, kasashe mambobin 'International Energy Agency' sun yanke shawarar sakin gangunan man fetur miliyan 400 daga ajiyarsu domin rage tasirin yakin a kasuwar makamashi.
Iran ta ruguza wa Amurka lissafi
Tun farko, an ji cewa Iran ta bayyana cewa Amurka ta yi tunanin za ta kai mata farmaki kuma cikin kankanin lokaci za ta murkushe ta amma sai ta ga akasin haka.
Babban sakataren Majalisar tsaro ta Iran, Ali Larijani ya lissafa abubuwa biyu da Amurka ta yi tsammani amma duka ba su samu ba.
Larijani ya kuma soki Shugaban Amurka, Donald Trump, kan maganarsa ta cewa Amurka za ta yi ruwa ta yi tsaki wajen zabar sabon jagoran Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
