Wata Sabuwa: Trump Ya Fadi Halin da Mojtaba Khamenei ke Ciki bayan Harin Isra'ila
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi jawabi kan halin da sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ke ciki a yanzu
- Khamenei bai fito bainar jama’a ba tun bayan zabensa a matsayin jagoran Iran bayan mutuwar mahaifinsa sai jiya Alhamis
- Sabon jagoran ya yi alkawarin ci gaba da rufe mashigar Hormuz tare da barazanar kai hari kan sansanonin Amurka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana halin da sabon jagoran addinin Musulunci a Iran ke ciki a yanzu.
Trump ya bayyana cewa yana ganin sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, na raye amma ya samu rauni.

Source: Twitter
A wata hira da aka yi da shi a shirin The Brian Kilmeade Show na gidan talabijin wanda New York Post ta bibiya, Trump ya ce yana ganin Khamenei na raye.

Kara karanta wannan
"Dole mu dauki fansa," Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya kada hantar Amurka da Isra'ila
Yadda aka zabi Mojtaba bayan kashe mahaifinsa
Mojtaba ya gaji mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka kashe a ranar farko ta yakin da Amurka da Isra'ila suka fara kai wa Iran.
Tun bayan da wani majalisar malamai ta zabe shi a karshen makon da ta gabata, ba a ga Mojtaba Khamenei a bainar jama’a ba.
Jawabinsa na farko da ya yi bayan hawansa kan mulki ma an karanta shi ne ta bakin wani mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na gwamnatin Iran.
A cikin jawabin farko da aka karanta, Mojtaba Khamenei ya yi alkawarin cewa Iran za ta ci gaba da rufe mashigar ruwa ta Hormuz.
Ya kuma bukaci kasashen makwabta su rufe dukkan sansanonin sojojin Amurka da ke kasashensu ko kuma su fuskanci harin Iran.

Source: Twitter
Martanin Trump kan halin da Khamenei ke ciki
Trump ya ce watakila yana raye kamar yadda ake fada amma kuma tabbas ya samu raunkuka sosai a harin da aka kai, cewar rahoton Reuters.

Kara karanta wannan
Mojtaba Khamenei: Sabon Jagoran Iran ya fadi abin da yake son kasashen Larabawa su yi wa Amurka
Ya ce:
“Ina ganin watakila yana raye. Ina ganin ya samu rauni, amma ina ganin har yanzu yana raye ta wata hanya.”
Yadda yakin Iran da Isra'ila ya barke
Amurka da Isra'ila sun fara kai hare-hare kan Iran tun ranar 28 ga Fabrairun shekarar 2026 wanda ya yi ajalin Ayatollah Ali Khamenei.
Tun daga lokacin, Iran ma ta mayar da martani da kai hare-hare kan Isra'ila da wasu kasashen yankin Tekun Fasha da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.
Yayin da yakin ke kusantar makonni biyu, rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da girgiza kasuwannin duniya da taba tattalin arzikin wasu kasashe.
Netanyahu ya tura kalubale ga Mojtaba Khamenei
An ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya dura kan sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bayan ya yi jawabi a kasar.
Netanyahu ya ce Khamenei ba zai iya fitowa bainar jama’a ba inda ya ce Amurka da Isra'ila na “murkushe” gwamnatin Iran da kungiyar Hezbollah.
Yayin jawabinsa, Mojtaba Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da kai hari kan sansanonin sojojin kasar Amurka a yankin gabas ta tsakiya.
Asali: Legit.ng