Yaki da Iran: Wani Babban Jirgin Dakon Man Amurka Ya Rikito daga Sararin Samaniya

Yaki da Iran: Wani Babban Jirgin Dakon Man Amurka Ya Rikito daga Sararin Samaniya

  • Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da bacewar jirgin dakon manta a yammacin Iraki yayin da ake gudanar da farmakin Epic Fury kan kasar Iran
  • Jami'an soji sun bayyana cewa ba wai harin makiya ne ya jawo bacewar jirgin ba, kuma ana cigaba da kokarin neman mutanen da ke cikinsa
  • Wannan ne jirgi na hudu da Amurka ta rasa a yakin Gabas ta Tsakiya bayan an kakkabo jiragen F-15 guda uku a kasar Kuwait bisa kuskure

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Rundunar sojojin Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa wani jirgin dakon mai nau'in KC-135 ya bace yayin gudanar da ayyukan soji a Iraki.

Jirgin ya bace ne a sararin samaniyar da ke karkashin ikon kawayen Amurka yayin gudanar da farmakin da sojojin suka sanyawa suna "Operation Epic Fury".

Kara karanta wannan

Trump ya fadi lokacin da zai dauki Amurka ta jefa kasar Iran cikin tsananin duhu

Wani babban jirgin dakon man amurka ya bace a sararin samaniya
Jirgin dakon man Amurka, kirar KC-135 da ya bace a sararin samaniyar Iraki. Hoto: JACK GUEZ / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Jirgin Amurka ya rikito daga samaniya

Sanarwar ta nuna cewa jirage biyu ne suka fuskanci wannan matsala, inda daya ya rikito kasa a yammacin kasar Iraki, yayin da na biyun kuma ya yi nasarar sauka lafiya ba tare da wata matsala ba, in ji rahoton Sky News.

Rundunar sojin ta nanata cewa faduwar jirgin ba ta da alaka da harin abokan gaba ko kuma kuskuren harbi daga dakarun kawance.

Farmakin "Operation Epic Fury" shi ne sunan da Amurka ta sanya wa hare-haren da take kai wa Iran tun daga ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa wadannan jirage na taka muhimmiyar rawa a yakin, musamman wajen samar da man fetur ga jiragen yaki a sararin samaniya domin ba su damar ci gaba da shawagi.

Yanayin jirgin Amurka da ya fado kasa

Jirgin KC-135 babban jirgi ne mai kama da na fasinja wanda kamfanin Boeing ya kera, kuma yana dauke da kwararrun ma'aikata akalla uku; matukin jirgi, mataimakinsa, da kuma mai kula da bututun loda man fetur.

Kara karanta wannan

Tsohon janar a gidan sojan Amurka ya bata yayin da yaki da Iran ke kara zafi

Sai dai wasu ayyukan na bukatar karin ma'aikata ko kuma fasinjoji har guda 37, kamar yadda rahoton NDTV ya nuna.

Wakilinmu Mark Stone ya bayyana cewa jirgi na biyu da ya sauka lafiya wani jirgin yaki ne wanda KC-135 din yake loda masa mai kafin hatsarin ya faru.

Wannan shi ne jirgi na hudu da sojin Amurka suka rasa tun farkon wannan yakin. Kafin wannan lokaci, an kakkabo jiragen yaki nau'in F-15 guda uku ta sararin samaniyar Kuwait bisa kuskure.

Ko da yake a lokacin matukan jirgin duka su shida sun yi nasarar fita kafin jiragen su fadi, wannan sabon hatsari ya sake tayar da hankula game da tsaron dakarun Amurka dake fagen fama.

Jirgin Amurka, KC-135 ya rikito daga sama ya fada kasa.
Jirgin Amurka, kirar KC-135, da ke dakon feture ga jiragen yaki. Hoto: Norbert Voskens/SOPA Images/LightRocket via Getty Images
Source: Getty Images

Halin da sojojin Amurka ke ciki

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton cewa kusan sojojin Amurka 150 ne suka jikkata tun farkon wannan rikici tsakanin hadakar Amurka da Isra'ila da kuma Iran.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto domin gano inda jirgin ya fadi da kuma halin da ma'aikatansa suke ciki.

Kara karanta wannan

Trump ya harzuka IRGC: Iran ta darkake jiragen dakon mai a cikin tekun Iraq

Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da dakarun Amurka ke fuskantar hare-hare daga jiragen yaki, makaman linzami, da kuma jirage marasa matuka na kasar Iran.

Jirgin daukar jiragen yakin Amurka ya kama da wuta

A wani lamari, mun ruwaito cewa, jirgin ruwan daukar jiragen yakin Amurka, USS Gerald R. Ford, ya gamu da gobara a cikin teku a ranar Alhamis.

Babban jirgin yana taimakawa a 'Operation Epic Fury' wanda Amurka da Isra'ila suka kaddamar ta hanyar kai hare-hare kan kasar Iran.

Hukumomi sun yi bayani game da ko tashin gobarar na da alaka da yakin da ake fafatawa, yayin da suka ce wasu sojoji sun jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com