Cin Kofin Duniya: Trump Ya Gargadi Kasar Iran kan Shiga Gasar a Amurka

Cin Kofin Duniya: Trump Ya Gargadi Kasar Iran kan Shiga Gasar a Amurka

  • Shugaban Donald Trump ya yi magana game da yiwuwar shigar tawagar kwallon kafa ta Iran gasar cin kofin duniya
  • Trump ya ce ba zai iya ba da tabbacin tsaron tawagar ta Iran ba idan ta zo Amurka domin fafatawa a gasar ta shekarar 2026
  • Ministan wasanni na Iran ya ce yakin Amurka da Isra'ila ya sa kasar ba za ta shiga gasar ba saboda hare-haren da aka yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da shigar Iran gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka.

Trump ya bayyana cewa ba zai iya ba da tabbacin tsaron tawagar kwallon kafa ta Iran ba idan ta je Amurka domin halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Yaki ya gigita Iran, ba za ta samu damar buga gasar cin kofin duniya ba a Amurka

Trump ya sake magana kan zuwan Iran gasar cin kofin duniya
Tawagar yan wasan kwallon kafa ta Iran da Shugaba Donald Trump. Hoto: Ibraheem Al Omari/Reuters, Donald J Trump.
Source: Facebook

Amurka: Trump bai da tabbacin tsaron 'yan Iran

Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social wanda a ranar Alhamis 12 ga watan Maris, 2026.

Ya ce tawagar Iran na maraba da shiga gasar kofin duniya, amma yana ganin bai dace su zo ba saboda lafiyarsu da tsaronsu da ake ganin yana cikin hatsari.

Ya rubuta cewa:

“Muna maraba da tawagar kwallon kafa ta Iran na shiga gasar kofin duniya, amma ban ga ya dace su zo ba saboda rayuwarsu da tsaronsu.”

A cewar rahotanni, an shirya Iran ta buga wasanni uku na rukuni a watan Yunin shekarar 2026 a biranen Amurka.

Wasannin sun hada da na karawa da New Zealand da Belgium a Los Angeles, da kuma wasa da Egypt a Seattle.

Trump ya ce bai da tabbacin tsaron yan Iran a Amurka
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka a birnin New York. Hoto: Donald J Trump.
Source: Twitter

Iran ta fasa shiga gasar cin kofin duniya

Sai dai ministan wasanni na Iran, Ahmad Donyamali, ya ce yakin da Amurka da Israel suka fara da Iran ya sa kasar ba za ta iya shiga gasar ba.

Kara karanta wannan

Iran ta yi martani ga barazanar Trump, ta magantu kan kawar da shi a doron kasa

Ya ce kashe babban jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da wasu manyan jami’an gwamnati ya sa ba zai yiwu kasar ta halarci gasar ba.

Donyamali ya bayyana cewa:

“Idan aka yi la’akari da cewa wannan gwamnati ta kashe jagoranmu, babu wani yanayi da zai sa mu halarci gasar kofin duniya da aka shirya yi a Amurka.”

Kasashen Amurka, Canada da Mexico ne za su karbi karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da za a yi tsakanin watan Yuni zuwa Yulin shekarar 2026.

Kofin duniya: Trump ya magantu game da Iran

A wani labarin, kun ji cewa kasar Iran ta yi nasarar shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 wadda za a fafata a kasashen Amurka, Canada da Mexico.

Yakin da ya barke tsakanin Amurka, Iran da Isra'ila, ya kawo kan yiwuwar kasancewar kasar a gasar wadda hukumar FIFA ke shiryawa duk bayan shekaru hudu a duniya.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana kan yiwuwar kasancewar Iran a gasar buga kwallon kafan yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.