Mojtaba Khamenei Ya Yi Jawabin Farko, Ya Faranta wa Wadanda Yakin Iran Ya Shafa
- Sabon jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei ya yi jawabin farko tun bayan nada shi mukami
- Nadin Mojtaba Khamenei na zuwa ne bayan kisan mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026
- Sabon jagoran ya sanar da tallafin kudi ga mutanen da gidajensu ko dukiyarsu ta lalace a hare-haren da aka kai a Iran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi jawabi a karon farko bayan nada shi mukamin jagoran addini a kasar.
Khamenei ya sanar da shirin tallafin kudi ga mutanen da gidajensu ko dukiyarsu ta lalace sakamakon hare-haren da ake kai wa kasar.

Source: Getty Images
A cikin wani jawabi da aka karanta a gidan talabijin na gwamnati, ya ce gwamnatin Iran za ta tallafa wa fararen hula da rikicin da ake ci gaba da yi ya shafa, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Mojtaba: Sabon Jagoran Iran ya fadi abin da yake son kasashen Larabawa su yi wa Amurka
Taimako da Khamenei ya Iraniyawa
Ya bayyana cewa tallafin zai hada da taimakon kudi ga wadanda gidajensu ko kadarorinsu suka lalace sakamakon hare-haren.
Haka kuma ya ce gwamnati za ta samar da kulawar lafiya ga mutanen da rikicin ya shafa domin rage wahalhalun da suke fuskanta.
A cewarsa, wannan na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin taimaka wa jama’a yayin da rikicin ke ci gaba.
Mojtaba Khamenei ya kuma bayyana cewa duk wanda ya ji rauni a hare-haren zai samu magani kyauta a asibitocin gwamnati.
Ya ce wannan mataki wani bangare ne na kokarin gwamnati na kula da wadanda rikicin ya jikkata da kuma tallafa musu wajen samun sauki.

Source: Twitter
Matakan da Mojtaba Khamenei ya dauka
Mojtaba Khamenei ya yi kira ga hadin kan kasa, yana mai cewa mashigar ruwa mai muhimmanci ta Hormuz, za ta ci gaba da kasancewa a rufe domin matsa lamba ga makiyan Iran.
Ya kara da cewa dukkan sansanonin sojin Amurka da ke yankin ya kamata a rufe su nan da nan, ko kuma za a kai musu hari.
Duk da cewa Iran na son zaman lafiya da makwabta, ya ce hare-hare kan sansanonin Amurka za su ci gaba.
Shugaban ya kuma ce kungiyoyin mayaka a Yemen “su ma za su yi aikinsu,” sannan ya kara da cewa mayaka a Iraq ma “na son taimaka wa juyin juya halin Musulunci.”
A karshe, Khamenei ya gode wa sojojin Iran, yana mai cewa su ne suka hana kasar ta fada karkashin iko ko kuma ta rabu-rabu yayin da take fuskantar hare-hare.
Iran ta sauya salon yaki da Isra'ila
Mun ba ku labarin cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da sauya dabaru da salon ka hare-hare a yakin da take da kasashen Amurka da Isra'ila.
Babbar hedkwatar sojojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta ce ta dakatar da tsarin kai hare-haren ramuyar gayya kan wadanda ta kira 'makiya'.
Ta kuma jaddada cewa daga yanzu za ta fara kai hare-hare kai tsaye kan Isra'ila da sansanonin Amurka, lamarin da ake ganin zai kara tsananta rikicin.
Asali: Legit.ng
