Isra'ila Ta Yi wa Iran Babbar Illa: An Hallaka Babban Kwamanda a Rundunar IRGC
- Sojojin Isra'ila sun hallaka Abu Dharr Mohammadi wanda shi ne babban jagoran dakarun Iran dake kula da sashin makamai masu linzami na Hezbollah
- An bayyana Mohammadi a matsayin mai shiga tsakanin Iran da Hezbollah wajen tsara hare-haren makamai masu linzami da rokokki zuwa cikin Isra'ila
- Firamista Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa dole ne Lebanon ta kawo karshen Hezbollah muddin tana son kauce wa hare-hare daga sojojin IDF
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lebanon - Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta tabbatar da kisan Abu Dharr Mohammadi, wani babban kwamandan gudanarwa a rundunar sojojin Iran ta IRGC.
Abu Dharr Mohammadi ya kasance kwamandan sashin makamai masu linzami na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran dake aiki a cikin ƙungiyar Hezbollah.

Source: Getty Images
Isra'ila ta hallaka wani kwamandan Iran

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
A cewar sanarwar da IDF ta fitar a shafinta na X, an hallaka Mohammadi ne a ranar Talata, inda aka bayyana shi a matsayin mutum mai muhimmanci wajen gina dabarun yaƙi da ƙarfafa makaman linzamin Hezbollah waɗanda ake amfani da su wajen kai wa Isra'ila hari.
Wannan kisan na zuwa ne a matsayin wani babban rauni ga tsarin haɗin gwiwar soji tsakanin Iran da ƙawayenta dake yankin Lebanon.
A cikin sanarwar, IDF ta bayyana cewa:
"A farkon wannan makon nan, dakarun sojin Isra'ila (IDF) sun yi nasarar kai hari tare da hallaka Abu Dharr Mohammadi, wani babban kwamanda a ƙarƙashin dakarun IRGC dake gudanar da ayyuka a sashin makaman linzami na ƙungiyar Hezbollah a birnin Beirut.
"Mohammadi ya kasance babban jigo wajen daidaita dabarun yaƙi tsakanin ƙungiyar Hezbollah da gwamnatin Iran, inda yake taka rawar gani a matsayin jagora kuma mai shiga tsakanin jami'an Hezbollah da na Iran."
Tasirinsa wajen farfaɗo da karfin makaman Hezbollah
Bugu da ƙari, Mohammadi ya kasance jagorawajen gina ƙarfin sojojin Hezbollah a fannin makamai masu linzami da rokokki, kamar yadda sanarwar IDF ta nuna.
Sanarwar ta ce ya yi aiki tuƙuru wajen farfaɗo da sashin makaman ƙungiyar bayan lahanin da suka samu sakamakon harin da Isra'ila ta kai musu a baya.

Kara karanta wannan
Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran
Rahotanni sun nuna cewa shi ne ya jagoranci matakai daban-daban na harba makamai masu linzami zuwa cikin ƙasar Isra'ila a yayin fafatawar da ake yi yanzu.
Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa hallaka shi zai kawo cikas ga yadda Hezbollah ke tsara hare-harenta na makamai masu linzami da rokokki.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Manufar Netanyahu kan dakarun Hezbollah

Source: Getty Images
Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya sake jaddada matsayinsa na cewa dole ne gwamnatin Lebanon ta tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2024 tare da lalata rundunar Hezbollah baki ɗaya.
Ya yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai sanya Lebanon fuskantar sakamako mai tsanani, ciki kuwa har da hare-hare kamar yadda take gani yanzu, in ji rahoton Times of Israel.
Shi ma Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya gargaɗi Lebanon cewa za ta "biya babban farashi" idan Hezbollah ta ci gaba da hare-harenta, ko da yake ya jaddada cewa Isra'ila ba ta da burin ƙwace filayen Lebanon.
Sojojin Isra'ila sun kashe fasto a Lebanon
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Isra'ila sun kashe wani limamin cocin Katolika, Pierre al-Rahi a Lebanon yayin da yake kokarin ceto wadanda hari ya raunata.

Kara karanta wannan
Trump na maganar kawo karshen yaki, Iran ta sake harba makamai masu hadari cikin Isra'ila
Fafaroma Leo XIV ya nuna alhini kan kisan limamin cocin tare da yin kira ga kasashen duniya da su gaggauta tsagaita bude wuta yanzu.
Uba al-Rahi ya ki tserewa daga kauyensa domin ya ci gaba da ba mabiyansa kariya ta addini kafin harin tankar yakin Isra'ila ya hallaka shi.
Asali: Legit.ng