Hare Haren Iran Sun Yi Wa Isra'ila Barna, an Bayyana Dubban Mutane da Aka Raunata
- Ana ci gaba da fafata yaki a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan kasar Iran
- Ma'aikatar lafiya ta kasar Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka raunata sakamakom hare-haren makamai masu linzami na Iran
- A cewar ma'aikatar, a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai mutane 179 da suka samu raunuka zuwa asibitoci domin duba lafiyarsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka samu raunaka sakamakon hare-haren da Iran ke kawo kasar.
Ma'aikatar lafiyar ta bayyana cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai mutane 179 da suka ji rauni zuwa asibitoci sakamakon rikicin da ake yi da Iran.

Source: Twitter
Jaridar Times of Israel ta kawo rahoton adadin mutanen da suka samu rauni sakamakon yakin a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.
Hare-haren Iran sun raunata mutane a Isra'ila
Adadin mutanen da suka raunata sakamakon hare-haren makamai masu linzami na Iran ya haɗa da fararen hula da kuma sojoji.
Daga cikin waɗanda ake yi wa magani a asibitoci, mutane huɗu suna cikin yanayi matsakaici, yayin da 157 suke cikin kyakkyawan yanayi.
An yi wa mutane 18 maganin fargaba da firgitar zuciya, tashar BBC Hausa ta kawo labarin.
Yayin da ma'aikatar ba ta ba da dalla-dallar abubuwan da suka janyo raunukan ba, ana kyautata zaton cewa akasarin raunukan mutane sun ji su ne yayin ƙoƙarin neman wuraren fakewa.
Ana ganin cewa ba a samu raunukan ba kai-tsaye daga makamai linzami na Iran ko harba rokoki da makamai masu linzami daga Lebanon.
Adadin mutanen da aka raunata a Isra'ila
Haka kuma ma'aikatar ta ce tun farkon fara yaƙi da Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, an kwantar da mutane 2,745 a asibitoci, waɗanda 85 daga cikinsu suna asibiti a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
Daga cikin waɗanda ke kwance a asibiti, mutane 11 suna cikin yanayi mai tsanani, mutane 10 suna cikin yanayi matsakaici, sannan 64 suna cikin kyakkyawan yanayi.
Isra'ila za ta ci gaba da kai hare-hare
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce aikin sojan zai ci gaba ba tare da wani kayyadadden lokaci ba.
Ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan Iran da mayakan Hezbollah a kasar Lebanon, har sai sun cimma dukkanin muradunsu.
"Za mu ci gaba da kai hare-hare muddin ana buƙata, har sai mun cimma dukkan manufofinmu kuma mun yi nasara a yaƙin”
- Israel Katz

Source: Twitter
Sojojin Isra'ila da suka ji rauni
Rundunar sojojin Isra'ilata ce an raunata sojojinta 14 tun farkon fara yaki da kasar Iran.
Daga cikin sojojin da aka raunata ciki har da guda shida a Kudancin Lebanon yayin da suke fafatawa da mayakan Hezbollah.
Rikici tsakanin Iran da Isra’ila ya ƙara tsananta a cikin kwanakin nan, inda ɓangarorin biyu ke ci gaba da kai hare-hare.
Lamarin da ke ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali da rudani saboda hare-haren da ake kai wa.

Kara karanta wannan
Iran ta sake harba makamai, ta yi wa yahudawa mummunar barna a Isra'ila cikin awanni 24
Harin Iran ya raunata sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa bayanai sun fito kan barnar da wani harin Iran ya yi a sansanin sojojin Amurka da ke kasar Iran.
Harin wanda ya kashe sojojin Amurka shida a sa’o’in farko na yaƙin da ake yi da Iran ya fi muni fiye da yadda aka bayyana.
Mutane da dama sun samu raunuka da suka haɗa da raunin ƙwaƙwalwa, raunukan shigar karfe, da ƙonewa a sakamakon harin.
Asali: Legit.ng
