Shugaban Amurka Ya Fara Fuskantar Matsala daga cikin Magoya Bayansa kan Yaki da Iran
- Magoya bayan Shugaban Amurka, Donald Trump sun fara tunanin cewa ya ci amanarsu saboda yadda ya jagoranci yaki da kasar Iran
- Fitaccen mai watsa shirye-shirye a Amurka, Joe Rogan, ya ce Trump ya yi alkawarin cewa kasar ba za ta sake shiga yaki ba lokacin kamfe
- Wannan na zuwa ne yayin da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ke kara zafi tun bayan fara kai hare-hare a karshen watan Fabrairu, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump sun fara dawowa daga rakiyarsa tun da ya kaddamar da hare-hare kan Iran.
Fitaccen mai watsa shirye-shirye na Amurka, Joe Rogan ya soki matakin Trump na kai hari kan Iran, yana cewa wasu daga cikin magoya bayan Shugaban kasar na tunanin an ci amanarsu saboda yakin.

Source: UGC
Magoya bayan Donald Trump sun fara zarginsa
Rogan ya bayyana haka ne a wani sabon shirinsa tare da marubuci Michael Shellenberger, wanda tashar NBC News ta Amurka ta watsa.
A cewar Rogan, wanda yana cikin wadanda suka goyi bayan dawowar Trump kan mulki, harin sojoji da Amurka ta kai Iran ya sabawa alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe.
“Wannan ne ya sa mutane da yawa suke jin an ci amanarsu. Ya yi takara da alkawarin cewa ba za a sake shiga yaki ba amma yanzu muna cikin wani yaki da ba mu san dalilinsa ba,” in ji Rogan.
Rogan ya kara da cewa yakin “kamar mahaukaci ne” saboda a ganinsa ba a fayyace manufar sa ba har yanzu.
Tsoron fadawa yakin duniya
A cikin shirin, Rogan ya kuma gargadi cewa karuwar wannan rikici a kan sauran rikice-rikice kamar yakin Gaza da yakin Ukraine na iya haifar da hadarin barkewar yakin duniya na uku.
Maganar Rogan ta kara nuna rabuwar kai a cikin magoya bayan Trump kan yakin Iran, yayin da gwamnatin Amurka ke ci gaba da kare matakin a matsayin kariya ga tsaron kasar, in ji rahoton Straight Arrow News.

Source: Getty Images
Fadar White House ta yi martani
Fadar gwamnatin Amurka ta kare matakin Trump, inda Mai magana da yawun White House, Anna Kelly, ta ce harin na daga cikin manufofin “Amurka farko” kuma an yi shi ne domin kare kasar daga barazanar gwamnatin Iran.
Ta ce gwamnatin Trump na kokarin hana Iran mallakar makamin nukiliya, rage karfin makamai masu linzami da dakile tallafin da take bai wa kungiyoyin da ke kai hare-hare a yankin.
Amurka ta gano halin da Iran ke ciki
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar leken asirin Amurka ta gano cewa har yanzu shugabannin Iran na nan daram kuma cikin hadin kai kuma suna da goyon bayan al'umma.
Rahoton ya nuna cewa duk da kashe tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei a ranar 28 ga Fabrairu, shugabannin addini da na siyasa a Tehran sun ci gaba da kasancewa cikin hadin kai.
Duk da yake hare-haren Amurka da Isra’ila sun kashe manyan jami’ai da kwamandojin IRGC da dama, tsarin gwamnatin kasar ta Musulunci bai rushe ba.
Asali: Legit.ng

