Trump Ya Harzuka IRGC: Iran Ta Darkake Jiragen Dakon Mai a cikin Tekun Iraq
- Wasu jiragen dakon mai guda biyu sun kama da wuta a tekun Iraki sakamakon hare-haren Iran wadanda suka jefa kasuwar makamashi cikin fargaba
- Iran ta yi gargadin cewa farashin danyen mai zai iya kai dala 200 sakamakon dagulewar tsaro da kasar Amurka ta haddasa a yankin Gabas ta Tsakiya
- Hukumar UNICEF ta tabbatar da cewa yara fiye da 1,000 ne suka mutu ko suka jikkata tun fara yakin, yayin da aka kashe fiye da mutum 1,200 a Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iraki - Wasu manyan jiragen dakon mai guda biyu ne suka kama da wuta a tekun Iraki yau Alhamis, sakamakon abin da ake zargin hare-haren ramuwar gayya ne daga ƙasar Iran.
Wannan harin shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da suka shafi wuraren makamashi da sufuri a faɗin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

Source: Getty Images
An samu karin mace mace a Gabas ta Tsakiya
Harin na zuwa ne jim kadan bayan sanarwar da hukumar makamashi ta duniya (IEA) ta bayar na fitar da adadi mai yawa na ɗanyen mai daga asusun ajiyar gaggawa domin rage raɗaɗin tsadar mai da ya addabi duniya, in ji rahoton Reuters.
Tun bayan fara wannan yaƙi kusan makonni biyu da suka gabata, wanda ya samo asali daga hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila kan Iran, mutane kusan 2,000 ne suka rasa rayukansu.
Hukumar UNICEF ta bayyana wani rahoton ban tausayi cewa yara fiye da 1,100 ne aka kashe ko aka raunata a cikin wannan ƙanƙanin lokaci.
Iran ta fitar da gargaɗi mai tsanani ga duniya cewa ta shirya tsaf domin ganin farashin mai ya kai dala 200 a kowace ganga, tana mai cewa tsaron yankin da Amurka ta dagula shi ne ya jawo hauhawar farashin man yau.
Iran ta darkake jiragen dakon mai a Iraki
Hare-haren yau sun haifar da gagarumin firgici a kasuwannin hannun jari na duniya, inda farashin ɗanyen mai ya sake haura dala 100 bayan ya tashi da kashi 10 a kasuwannin Asiya.
Masana sun bayyana cewa wannan hari na Iran kusan nuna yatsa ne ga shirin Amurka na fito da mai daga rumbunta zuwa kasuwa domin saukaka farashin da ya tashi sama.
A lardin Basra na ƙasar Iraki, hukumomi sun tabbatar da cewa jiragen da aka farmaka sun kasance suna gudanar da sauya mai ne daga wannan jirgi zuwa wancan lokacin da lamarin ya faru.
Wannan ya tilasta wa Iraki dakatar da ayyuka na ɗan lokaci a manyan tashoshin fitar da mai na kudancin ƙasar yayin da ake tantance irin barnar da aka samu, in ji rahoton Aljazeera.

Source: Getty Images
Kalaman Trump da hare-haren Iran
Ma'aikatar man fetur ta Iraki ta bayyana cewa duk wani hari kan jiragen ruwa babban barazana ne ga tattalin arzikin ƙasar, ganin cewa kusan daukacin kuɗaɗen shigar Iraki sun dogara ne kan fitar da mai ta waɗannan tashoshin.
A yayin wani taron yaƙin neman zaɓe a Kentucky, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta riga ta ci nasara a yaƙin, amma ya jaddada cewa ba sa son janyewa da wuri domin guje wa komawa bayan kowace shekara biyu.
Sai dai, wani hari kan jiragen dakon mai, da kuma barazanar cewa man zai koma dala 200 na ci gaba da sanya fargaba a zukatan ƙasashen da suka dogara ga shigo da mai, ciki har da ƙasashen Afirka.
Kalli bidiyon harin wanda Middle East Eye ta wallafa a shafinta na Facebook a kasa:
Makamin Iran ya daki birnin Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, sababbin hare-haren makaman linzami daga Iran sun girgiza birnin Tel Aviv inda mutane biyu suka mutu, wasu suka jikkata.
Ita ma kungiyar Hezbollah ta doki wata makarantar renon yara a Isra'ila inda mutane 14 suka jikkata yayin da ake tsaka da fafata wannan yaki.
Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa babban burin wannan yakin shi ne kawo ƙarshen mulkin Jamhuriyar Musulunci gaba ɗaya a kasar Iran.
Asali: Legit.ng

