Yakin Iran: Gazawar Isra'ila Ta Fito, Netanyahu Ya Fara Korafi kan Rashin Kudi

Yakin Iran: Gazawar Isra'ila Ta Fito, Netanyahu Ya Fara Korafi kan Rashin Kudi

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana game da yakin da ya hada kai da Amurka suka fara a Iran a karshen watan Fabrairun 2026
  • Netanyahu ya yi maganar da ke nuna alamar damuwa da yawan kudin da za a bukata wajen cigaba da yaki da Iran, lamarin da ya girgiza Isra'ila
  • Firaministan ya fadi haka ne yayin da rahotanni da dama ke nuna cewa Amurka na kashe makudan kudi a yaki da Iran, lamarin da Amurkawa ke suka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Isra'ila - Bayan shafe kusan mako biyu ana gwabzawa, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nuna cewa kashe makudan kudi wajen yaki da Iran zai girgiza su.

Maganar Benjamin Netanyahu ta zo ne a daidai lokacin da Iran ke cigaba da kai hare-hare Isra'ila da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Amurka da Iran ya jefa gwamnatin Donald Trump a fargaba

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a wani taro da ya halarta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Duk da makudan kudin da ya ce za a kashe, Middle East Monitor ta rahoto cewa Netanyahu ya bayyana cewa shiga yakin ya zama musu dole.

Me ya girgiza Benjamin Netanyahu kan Iran?

Netanyahu ya amince cewa yaki da Iran zai janyo gagarumin kashe kudi, yana mai cewa gwamnati za ta bukaci ware wani kasafin kudi na musamman na lokacin yaki wanda ya kai daruruwan biliyoyi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar tare da ministan kudin Isra’ila, Bezalel Smotrich, a yammacin ranar Talata, Netanyahu ya ce gwamnati ta dauki yakin a matsayin abin da ba za a iya kauce masa ba.

Duk da haka, Firaminista Netanyahu ya yi gargadin cewa tarin kudin da za a kashe zai kasance mai yawa ga kasar Yahudawar ta Isra'ila.

Ya ce:

“Babu shakka cewa dole ne mu yi wannan yaki, kuma muna yin duk mai yiwuwa tare da sojojinmu da matukan jiragen yaki.”

Kara karanta wannan

Trump ya sake maganar kawo karshen yaki da Iran, ya yi wa duniya albishir

Kamar yadda jaridar Haaretz ta Isra’ila ta rahoto, Netanyahu ya kara da cewa:

“Amma akwai babbar matsala guda daya: yana da tsada, tsada matuka. Saboda haka dole ne mu ware wani kasafin kudi na musamman a lokacin yaki, wanda ya kai daruruwan biliyoyi, domin tallafa wa kasafin kudin tsaro da kuma kokarin yaki.”
Benjamin Netanyahu da Donald Trump
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar Ministan kudin Isra'ila

Ministan kudin Isra’ila, Bezalel Smotrich, ya tabbatar da cewa karin kudin da za a kashe zai kai daruruwan biliyoyi, yana mai cewa hakan sadaukarwa ne da za su yi.

Smotrich ya kuma nuna cewa gwamnati za ta dakatar da tattaunawa kan wasu muhimman batutuwan cikin gida na wani lokaci domin mayar da hankali kan yaki da Iran.

Daya daga cikin matakan da za a jinkirta shi ne wani kudirin doka da ya shafi kebe Yahudawan Orthodox daga aikin soja, wanda a baya ya haifar da muhawara mai zafi a siyasar Isra’ila.

Isra'ila ta taba farmakar Amurka a 1967

A wani labarin, kun ji cewa a shekarar 1967 dakarun Isra'ila suka kai mummunan farmaki kan jirgin ruwan sojojin Amurka suna tafiya a teku.

Kara karanta wannan

Shugaban Trump ya canza magana, ya hango karshen yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Tarihi ya nuna cewa sojojin Isra'ila sun shafe sa'o'i suna sakin makamai kan jirgin, lamarin da ya jawo mutuwar sojoji da fararen hula sama da 30.

Bincike ya tabbatar da cewa harin yana cikin mafi munin abin da ya faru da dakarun Amurka kasancewar sojoji da dama sun jikkata a farmakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng