Gaskiya Ta Fito, Shugaba Macron Ya Sabawa Trump kan Yakin Amurka da Iran
- Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce har yanzu sojojin Iran suna da ragowar karfi duk da Amurka da Isra'ila sun masu illa
- Macron ya bayyana haka ne a wani taron shugabannin kungiyar G7, wanda aka gudanar ta intanet yau Laraba, 11 ga watan Maris, 2026
- Wannan kalamai na Macron na zuwa ne awanni 24 bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa sun murkushie duk wani karfin sojojin Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
France - Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra'i'a sun yi wa kasar Iran mummunar illa a bangaren karfin sojanta.
Sai dai duk da haka, Shugaba Macron ya tabbatar da cewa ba a mukushe sojojin Iran gaba daya ba, har yanzu suna da ragowar kargi a fafatawar da ake a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun sha mamaki, an gano abin da Iran ke amfani da shi a musayar wuta

Source: Getty Images
Macron ya sabawa Shugaba Trump
A rahoton da tashar Al-Jazeera ta kawo, ta ce Shugaba Macron ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan wata tattaunawa ta bidiyo da shugabannin kasashen kungiyar G7.
Wannan kalamai na Macron na zuwa ne awanni 24 bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa sun murkushe duk wani karfin sojojin Iran.
Da gaske an murkushe karfin sojojin Iran?
Amma da yake jawabi a taron G7, wanda Shugaba Trump ya halarta, Macron ya ce duk da cewa hare-haren sun lalata wani bangare mai muhimmanci na makaman Iran, har yanzu kasar na da damar kai farmaki.
“An riga an yi babbar illa ga karfin makamai masu linzami na Iran, amma har yanzu tana kai hare-hare kan wasu kasashe a yankin. Don haka ba za a ce karfinta ya kare gaba daya ba,” in ji shi.
Macron ya bukaci Trump ya fadi manufarsa

Kara karanta wannan
Yaki da canza salo, Iran ta sauya dabarun kai hare hare kan sansanonin Amurka da Isra'ila
Shugaban na Faransa ya kuma ce ya bar wa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana manufar karshe ta yakin da kuma yadda yake son tafiyar da hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci.
Macron ya ce Trump ne zai iya fayyace menene burin karshe na yakin, da kuma hanzarun da ake bukata nan gaba wajen kaddamar hare-haren kan Iran, in ji rahoton Vanguard.
A yau Laraba, 11 ga watan Maris, 2026 aka shiga rana ta 12 da fara yakinm Amurka/Isra'ila da kasar Iran, lamarin da ya yi ajalin daruruwam mutane da jikkata dubbai.

Source: Getty Images
Koriya ta Kudu ta goyi bayan kasar Iran
A wani rahiton na daban, kun ji cewa Koriya ta Arewa ta shiga sahun kasashen duniya da suka yi magana game da yakin da ake cigaba da yi tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ta ya caccaki Amurka da Isra'ila a kan fara kai hare-hare Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 da ya jawo kashe mutan ciki har da jagoran addini, Ali Khamenei.
Gwamnatin Kim Jong Un ta goyi bayan nadin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin Iran bayan kashe mahaifinsa a harin Amurka/Isra'ila
Asali: Legit.ng