"Sai an Cika Su"; Iran Ta Kafa Sharuddan Kawo Karshen Yaki da Amurka, Isra'ila
- Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare kan kasar Iran, yayin da take mayar da martani a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasarsa na son ganin an samu zaman lafiya a yankin
- Masoud Pezeshkian ya gindaya sharudda guda uku da za su sanya a kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana kan kawo karshen yakin kasarsa da Amurka da Isra'ila.
Masoud Pezeshkian ya lissafa sharuɗɗa guda uku da ƙasarsa ke buƙata domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi yanzu da Amurka da Isra’ila.

Source: Getty Images
Masoud Pezeshkian ya lissafa sharuddan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026.
Shugaban na Iran ya ambaci ɗaya daga cikin sharuɗɗan a matsayin “biyan diyyar asara” da Amurka za ta yi na barnar da ta haddasa wa Iran.
Shugaban Iran ya tattauna da takwarorinsa
Ya ce ya bayyana waɗannan sharuɗɗan ne a tattaunawar da ya yi da shugabannin Rasha da Pakistan. ƙasashe biyu da suka yi Allah-wadai da Amurka da Isra’ila kan fara yaƙin.
Shugaban na Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce Tehran tana nan bakanta wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin, amma ya dage kan cewa yaƙin zai ƙare ne kawai idan aka amince da hakkokin kasarsa.
A cikin saƙonsa, Pezeshkian ya ce ya tattauna da shugabannin Rasha da Pakistan inda ya jaddada matsayin Iran na cewa wannan rikicin “gwamnatin Isra'ila da Amurka ne suka rura wutar sa”.
Wadanne sharudda Iran ta gindaya?
Ya ce duk wata maslaha dole ne ta haɗa da amincewa da haƙƙoƙin Iran, biyan diyya na asara, da kuma tabbaci na ƙasa da ƙasa wajen hana kai hare-hare a nan gaba.
“Yayin tattaunawa da shugabannin Rasha da Pakistan, na jaddada aniyar Iran na tabbatar da zaman lafiya a yankin."
"Hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen wannan yaƙi wanda gwamnatin Isra'ila da Amurka suka rura wuta, ita ce amincewa da halastattun haƙƙoƙin Iran, biyan diyya, da kuma ƙwaƙƙwaran tabbaci daga ƙasa da ƙasa kan hana duk wani hari a nan gaba.”
- Masoud Pezeshkian

Source: Getty Images
Iran na ci gaba da kai hare-hare
Duk da cewa Amurka ta ce ta lalata dukkan dakarun sojojin sama da na ruwan Iran, da kuma kusan dukkan ƙarfin makaman linzamin ƙasar, Iran tana ci gaba da harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan Isra’ila da sansanonin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma Iran ta tabbatar da rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, inda kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur ɗin duniya ke bi ta wurin, lamarin da ya haddasa ƙarin farashin fetur a faɗin duniya, ciki har da Najeriya.
Iran ta yi wa sojojin Amurka barna
A wani labarin kuma, kun ji cewa bayanai na ta fitowa kan barnar da Iran ta yi wa sojojin Amurka a harin da ta kai a Kuwait.
Majiyoyi sun bayyana cewa harin wanda aka kai ta hanyar amfani da jirgi mara matuki, ya yi barna mai girma.
Wasu daga cikin sojojin da harin ya ritsa da su sun samu munanan raunuka ciki hada wadanda suka shafi kwakwalwa.
Asali: Legit.ng

