Amurka da Isra'ila Sun Sha Mamaki, An Gano Abin da Iran ke Amfani da Shi a Musayar Wuta
- Ana zargin kasar Iran tana amfani da tauraron dan adam na BeiDou, wanda ke karkashin ikon kasar China, a yakinta da Amurka/Isra'ila
- Tsohon daraktan leken asiri na Faransa, Alain Juillet ya ce hare-haren da Iran kai kai wa a wannan karon na samun wuraren da aka hara
- Har yanzu babu wata sanarwa da ke nuna Iran na amfani da tsauraron dan adam na China, amma masana na ganin alamu sun tabbatar da hakan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Masana harkokin leken asiri sun ce akwai yiwuwar Iran na amfani da tsarin tauraron dan adam na kasar China mai suna 'BeiDou Navigation Satellite System'.
A cewarsu, Jamhuriyar Musulunci na amfani da wannan na'ura ta zamani ne domin kai hare-hare kan kadarori da kayayyakin Isra'ila da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Yaki da canza salo, Iran ta sauya dabarun kai hare hare kan sansanonin Amurka da Isra'ila

Source: Getty Images
Makaman Iran sun samu karfin saiti
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa tsohon daraktan leken asiri na Faransa, Alain Juillet, ya ce makaman Iran sun kara samun daidaito da saiti a yanzu idan aka kwatanta da yakin da aka yi watanni takwas da suka gabata.
Ya ce wannan ya sa masana ke tambayar wace irin fasahar jagorantar makamai Iran ke amfani da ita.
“Abin mamaki a wannan yakin shi ne yadda makaman Iran suka fi daidaito da samun wuraren da aka aika su idan aka kwatanta da yakin da ya faru watanni takwas da suka wuce,” in ji Juillet.
Yadda Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya
Bayan hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu 2026, Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuki zuwa Isra'ila da sansanonin sojin Amurka a kasashen Gulf.
Ko da yake kasashen Isra'ila da na Gulf sun kakkabo yawancin makaman, wasu sun samu nasarar tsallake kariya, wanda ya haddasa lalacewar kadarori da asarar rayuka, cewar raoton NBC News.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100
A baya, sojojin Iran sun fi dogaro da tsarin Global Positioning System (GPS), wanda masana suka ce Amurka na iya katsewa ko hana amfani da shi saboda mallakinta ne.
Amma idan Iran na amfani da tauraron dan adam na BeiDou, Amurka ba za ta iya kutse ko katse sabis din amfani da shi cikin sauki ba.
Mene ne BeiDou?
BeiDou Navigation Satellite System tsarin tauraron dan adam ne da China ta kirkira domin yin gogayya da GPS na kasar Amurka.
Shugaban kasar China, Xi Jinping, ne da kansa ya kaddamar da sabon tauraron dan adam din a shekarar 2020 a birnin Beijing.
China ta fara kirkirar tsarin ne bayan rikicin Taiwan na 1996, lokacin da ta ji tsoron cewa Amurka za ta iya katse damar amfani da GPS.

Source: Getty Images
Har yanzu gwamnatin Iran ba ta tabbatar da amfani da BeiDou ba, kuma ba ta yi karin bayani kan lamarin ba.
Sai dai wasu masana na ganin cewa idan Iran ta koma amfani da tsarin na China, hakan na iya nuna karshen karfin ikon Amurka kadai a fannin bayanan tauraron dan adam a fagen yaki.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
Harin Iran ya jikkata 'dan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa harin da Amurka ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu 'yan kasashe daban-daban.
Hukumomin UAE sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu na ci gaba da kakkabo makamai da jirage marasa matuki da Iran ke harbawa.
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce hare-haren Iran sun yi sanadin mutuwar mutane shida, wadanda suka hada da ‘yan asalin UAE, Pakistan, Nepal da Bangladesh.
Asali: Legit.ng