Djibouti: An Gano Wani Sansanin Sojan Amurka da Iran Za Ta Iya Farmaka a Afrika

Djibouti: An Gano Wani Sansanin Sojan Amurka da Iran Za Ta Iya Farmaka a Afrika

  • Ofishin jakadancin Amurka a Djibouti ya ba da sanarwar tsaro ta gaggawa sakamakon fargabar harin Iran kan sansanin sojin Camp Lemonnier
  • Camp Lemonnier shi ne ne kaɗai babban sansanin sojin Amurka na din-din-din a nahiyar Afrika wanda ake ganin zai iya fuskantar harin Iran
  • Sansanin na dauke da sojojin Amurka fiye da 4,000, kuma yana kusa da Yemen, inda Iran kan iya amfani da ƴan tawayen Houthi don kai masa hari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Djibouti - Hankula sun tashi matuƙa game da tsaron Camp Lemonnier, wanda shi ne kaɗai babban sansanin sojin Amurka na din-din-din a nahiyar Afrika.

Sansanin yana kusa da mashigar Bab el-Mandeb, wata hanya mai muhimmanci ga kasuwancin duniya da ake jigilar kashi 12 na dukkan kasuwancin duniya ta cikinta.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sanatocin Amurka sun kunnowa Trump wata wuta kan yaki da Iram

Iran na iya farmakar Camp Lemonnier, wani sansanin sojojin Amurka da ke a Afrika.
Wani sojan Amurka ya na shiga Camp Lemonier, sansanin sojojin Amurka da ke a Djibouti. Hoto: PEDRO UGARTE/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Fargabar harin Iran a sansanin Amurka

Sakamakon hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kai wa wurare da sansanonin Amurka a yankin Gulf, akwai fargabar cewa wannan sansanin na iya zama abin hari na gaba, in ji rahoton BBC Africa.

Ofishin Jakadancin Amurka a Djibouti ya fitar da sanarwar tsaro ta gaggawa yau, 11 ga Maris, inda ya soke dukkan ayyukan ofishin tare da shawartar ma'aikatansa da su guji zirga-zirga a kusa da Camp Lemonnier.

Wannan sansanin, wanda ke dauke da sojojin Amurka fiye da 4,000, yana kasa da mil 100 daga kasar Yemen, inda ƴan tawayen Houthi ke da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi waɗanda Iran ke ba daukar nauyinsu.

Tasirin rikicin kan tattalin arzikin Afrika

Masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa duk wani tashin hankali a wannan yankin zai shafi Afrika kai-tsaye fiye da sauran sassan duniya.

Ga hanyoyin da hakan zai faru:

Kara karanta wannan

Bayan jawo tashin fetur, rikicin Gabas ta Tsakiya ya kara jefa 'yan Najeriya a matsala

  • Hauhawar Farashin Man Fetur: Farashin ɗanyen mai ya haura dala 100 a kasuwar duniya kafin ya sauka. Tun da yawancin ƙasashen Afrika masu shigo da mai ne, wannan zai haifar da ƙarin kuɗin sufuri da wutar lantarki a birane kamar Legas da Nairobi.
  • Tsadar Abinci: Mashigar Bab el-Mandeb ita ce hanyar da ake biyo da kayan abinci kamar alkama, shinkafa, da sukari zuwa Afrika. Toishe wannan hanyar na nufin jinkiri da ƙarin kuɗin jigila, wanda zai sa farashin abinci ya tashi.
  • Barazanar Tsaro: Bayan Djibouti, yankin Somaliland ma na iya zama abin hari yana karɓar baƙuncin sansanin sojin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a Berbera, wacce abokiyar adawar Iran ce.
Ana fargabar Iran na iya farmakar sansanin sojojin Amurka na Camp Lemonier da ke Afrika.
Wata motar sojoji tana fita daga sansanin Camp Lemonier, wanda ke a Djibouti. Hoto: PEDRO UGARTE/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Abin da masana suka ce kan lamarin

Hubert Kinkoh, wani babban mai bincike, ya bayyana cewa Afirka tana fuskantar "haɗari" sakamakon wannan yaƙin saboda kusancinta da mashigar ruwa da kuma dogara ga man fetur daga ƙasashen waje.

A cewar rahoton RFI, Kinkoh ya bayyana cewa:

"Shigo da makamashi, zaman sansanonin sojojin kasashen waje, da kuma kasancewarta kusa da mashigar ruwa na nufin cewa yakin Gabas ta Tsakiya zai iya shafar Afrika a kankanin lokaci."

Yayin da Amurka ke biyan Djibouti dala miliyan 63 duk shekara domin zaman wannan sansanin, farashin da talakan Afrika zai iya biya a kasuwa sakamakon wannan yaƙin ya ninka hakan sau dubun dubata.

Sojan Amurka ya mutu a Saudiyya

A wani labari, mun ruwaito cewa,an sanar da mutuwar wani sojon Amurka a kasar Saudiyya bayan makaman da Iran ta harba sun masa mummunar illa.

Rundunar sojojin Amurka ta sanar da cewa a ranar 1 ga watan Maris 2026 ne Iran ta kaddamar da hare-hare kan sansanin da suke zaune.

An sanar da mutuwar sojan ne 'yan sa'o'i bayan Donald Trump ya karbi gawar wasu dakarun sojojin Amurka shida da Iran ta kashe a Kuwait.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com