Yaki Ya Gigita Iran, ba Za Ta Samu Damar Buga Gasar Cin Kofin Duniya ba a Amurka
- Ministan wasanni na Iran ya ce kasar ba za ta halarci gasar cin kofin duniya da za a yi ba bayan harin Amurka da Isra'ila
- Tehran ta ce kashe jagoranta, Ayatollah Ali Khamenei, ya sa ba zai yiwu kasar ta shiga gasar kwallon kafa ta duniya ba
- Duk da haka shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya ce Donald Trump ya ce yana maraba da tawagar Iran a gasar kwallon
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Gwamnatin kasar Iran ta yi karin haske kan ci gaba da yaki da ake yi a Gabas ta Tsakiya da ka iya shafar harkokin wasanni.
Kasar Iran ta bayyana cewa ba za ta halarci gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 ba bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan kasar.

Source: UGC
Abin da zai hana Iran zuwa kofin duniya
Ministan wasanni na Iran, Ahmad Donyamali, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na gwamnatin kasar, cewar gidan talabijin Al Jazeera.
Ya ce kashe jagoran addini kuma babban jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei, ya sa ba zai yiwu Iran ta shiga gasar ba.
A cewarsa:
“Idan aka yi la’akari da cewa wannan muguwar gwamnati ta kashe jagoranmu, babu wani yanayi da zai sa mu halarci gasar kofin duniya.”
Ana sa ran Amurka za ta karbi bakuncin gasar tare da Canada da Mexico, amma duk wasannin rukuni na Iran an shirya su ne a biranen Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa yakin da Amurka da Isra'ila suka fara kai wa Iran tun ranar 28 ga Fabrairun 2026 ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 1,200 tare da jikkata dubban mutane.
Iran ma ta mayar da martani da harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki kan Isra'ila da kuma wasu sansanonin sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ministan ya ce halin da ake ciki ya sa ‘yan kasar ba su cikin tsaro, wanda hakan ya sa halartar gasar ba zai yiwu ba, cewar Sky News.

Source: Getty Images
Abin da Shugaban FIFA ya ce kan Iran
Sai dai shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya jaddada cewa yana maraba da tawagar Iran ta shiga gasar.
Infantino ya bayyana cewa an tattauna batun ne yayin wata ganawa da Trump kan shirye-shiryen gasar da za a gudanar a watan Yuni zuwa Yulin 2026.
Iran ita ce kasa ta farko da ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026, wacce za ta gudana daga ranar 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yulin 2026.
Kofin duniya: Trump ya magantu game da Iran
Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta cancanci shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 wadda za a fafata a kasashen Amurka, Canada da Mexico.
Yakin da ya barke tsakanin Amurka, Iran da Isra'ila, ya kawo kan yiwuwar kasancewar kasar a gasar wadda hukumar FIFA ke shiryawa.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi magana kan yiwuwar kasancewar Iran a gasar buga kwallon kafan yayin da ake ci gaba da yaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

