Rasha Ta Yi Magana game da Zargin Tallafawa Iran, Ta Fadi Gaskiya kan Alakarsu
- Majiyoyi sun bayyana cewa kasar Rasha ta yi martani game da zarginta da ake yi da ba da bayanan sirrin sojojin Amurka
- Maganar ta fito ne bayan tattaunawar waya tsakanin Shugaba Donald Trump da shugaban Rasha, Vladimir Putin
- Rahoto ya zargi Moscow da bai wa Tehran bayanan wuraren jiragen ruwan yaki da jiragen sama na sojojin Amurka a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Moscow, Russia - Kasar Rasha ta yi martani game da zargin tana taimaka wa Iran da bayanan sirri domin yakar Amurka.
Kasar Rasha ta musanta rade-radin cewa tana taimaka wa Iran da bayanan sirri kan wuraren da kadarorin sojojin Amurka suke a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Jakadan musamman na Amurka, Steve Witkoff, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da jaridar CNBC.
Zargin da Amurka ke yi wa Rasha
Witkoff ya ce an bayyana wannan zargin ne yayin wata tattaunawar waya tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump, da shugaban Rasha, Vladimir Putin a ranar Litinin 9 ga watan Maris, 2026.
A baya dai jaridar The Washington Post ta ruwaito cewa Rasha na ba Iran bayanan kai hari da suka hada da wuraren da jiragen ruwan yaki da jiragen saman sojojin Amurka suke a Gabas ta Tsakiya.
Sai dai Witkoff ya ce Rasha ta karyata wannan zargi yayin tattaunawar da aka yi da shugaban Amurka.
A cewarsa:
“Jiya yayin tattaunawar waya da shugaban ƙasa, Rasha ta ce ba ta ba da irin waɗannan bayanai ba.
“Za mu iya ɗaukar maganarsu a matsayin gaskiya. Amma dai sun faɗi hakan. Haka kuma jiya da safe ni da Jared Kushner mun yi wata tattaunawa ta daban da mai ba Kremlin shawara kan harkokin waje, Yuri Ushakov, wanda shi ma ya sake jaddada irin wannan magana.”

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Source: Getty Images
Abin da Amurka ke gani kan martanin Rasha
Ya kara da cewa Amurka za ta iya daukar maganar Rasha a matsayin gaskiya, amma har yanzu ana sa ran hukumomin leken asiri su kara bincike kan lamarin.
Witkoff ya ce shi da Jared Kushner sun kuma yi wata tattaunawa ta daban da mai ba shugaban Rasha shawara kan harkokin waje, Yuri Ushakov.
Ya bayyana cewa Ushakov ma ya sake jaddada cewa Rasha ba ta ba da irin wadannan bayanai na sirri da Iran ba.
Duk da haka, Witkoff ya ce batun ya fi dacewa hukumomin leken asiri su tantance shi, yana mai cewa ana fatan Rasha ba ta ba da bayanan da Iran ba.
“Wannan tambaya ce da ta fi dacewa a yi wa jami’an leken asiri, amma muna fatan ba sa raba irin waɗannan bayanai.”
- Steve Witkoff
Putin ya tattauna da takwaransa na Iran
Kun ji cewa shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya kira waya inda suka tattauna da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian kan yakin da ake yi.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Putin ta tattauna da Pezeshkian kan yakin Iran da Isra'ila mai goyon bayan kasar Amurka.
Fadar Kremlin ta ce yayin tattaunawar, Putin ya jaddada matsayinsa na goyon bayan dakatar da rikicin da wuri domin rage tashin hankali.
Asali: Legit.ng

