Yadda Yakin Iran da Amurka Zai Shafi Ibadun Watan Ramadan, Umrah da Aikin Hajjin 2026

Yadda Yakin Iran da Amurka Zai Shafi Ibadun Watan Ramadan, Umrah da Aikin Hajjin 2026

Saudi Arabia - Yayin da rikice-rikice ke ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya, an fara nuna damuwa kan yiwuwar tasirin da hakan zai iya yi ga muhimman ibadun addinin Musulunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Hakan na zuwa ne bayan yaki ya barke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Amurka da Isra'ila, lamarin da ya jefa gaba daya yankin cikin tashin hankali.

Shugaban Amurka da Khamenei.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da tsohon jagoran addiinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: @DonaldJTrump, Anadolu
Source: Getty Images

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa Amurka da Isra'ila ne suka fara kai farmaki kan Iran, yayin da ita kuma ta maida martani da makamai masu linzami, lamarin da ya taba wasu kasashen Gulf ciki har da Saudiyya.

Fargabar tasirin yakin Iran ga Musulmi

Wannan yaki da ake ganin yana kara zafafa a kowane rana tun bayan fara shi a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026, ya haifar da fargaba kan yiwuwar ya shafi azumin Ramadan, Umrah da shirye-shiryen Hajjin 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Edogan ya yi gargadi da ya hango gagarumar matsala a yakin Iran da Amurka

Duk da cewa Saudiyya ta dade tana kokarin tabbatar da tsaro a biranen masu tsarki na Makkah da Madinah har a lokacin rikice-rikicen yankin, masana suna gargadin cewa wannan yaki na iya shafar Hajji da Umrah.

Saudiyya na daya daga cikin kasashen yankin Gulf da Iran ta kai wa hari, a wani mataki na ramuwar gayya kan hare-haren Amurka, sai dai hakan ya kawo tsaiko a abubuwa da dama a kasar.

Yadda zuwa Umrah ke karuwa a Ramadan

A wurin Musulmi, Ramadan ba kawai watan azumi ba ne; lokaci ne na ƙara ibada da neman kusanci da Allah SWT.

A wannan lokaci ne kuma mutane da dama ke tafiya zuwa ƙasar Saudiyya domin yin Umrah, wato ƙaramar hajji da ake iya yi a kowane lokaci na shekara.

Musamman a kwanaki 10 na ƙarshe na Ramadan, ana samun karuwar musulmi da ke son yin ibada a Masallacin Harami da Masallacin Annabi a Madinah.

Ka'ada.
Musulmi daga sassa daban-daban na duniya na gudanar da Umrah a Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Abubuwan da za su kawo cikas ga Musulmi

A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari kan rikicin Iran da Amurka/Isra'ila da kuma yadda yakin zai iya taba ibadun watan Ramadan, Umrah da aikin Hajjin bana da aka fara shirye-shirye.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila

1. Matsalar tsaro da kwanciyar hankali

Duk da cewa Saudiyya ta zuba jari sosai wajen inganta tsaro domin kare biranen masu tsarki da alhazai, amma wannan yaki da ke gudana tsakanin Iran da Isra'ila na iya zama babbar barazana ga kasar.

Duba da hare-haren da iran ta kai kan wasu muhimman wurare a Saudiyya, wadanda ta ce suna da alaka da Amurka, ana ganin wannan rashin kwanciyar hankali na iya taba aikin Umrah da Hajji.

A wani rahoto da jaridar Punch ta tattaro, daruruwan musulmin Najeriya sun rasa damar tafiya Saudiyya domin gudanar da Umrah a watan Ramadan saboda yakin Iran, Isra'ila da Amirka.

Wasu daga cikin musulmin sun bayyana cewa sun samu biza kuma an tsara za su tashi daga Najeriya zuwa Saudiyya a tsakanin, 4 zuwa 6 ga Maris,2026 amma saboda wannan yaki da ya barke, aka soke tafiyar.

2. Dakatar da sufurin jiragen sama

Daya daga cikin abubuwan da za su kawo cikas ga aikin Hajji da Umrah, kuma su taba ibadun da musulmi ke yi a watan Ramadan shi ne matsalar sufuri.

Kara karanta wannan

Lamari ya rincabe: Saudiyya ta gaji da shiru, ta gargadi Iran kan hare-harenta

Galibin kasashen Gabas ta Tsakiya sun dakatar da harkokin sufurin jiragen sama tare da rufe sararin samaniyarsu saboda halin tashin hankali da musayar wutar da ake yi tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila.

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa hakan ya shafi musulmin da ke shirin zuwa Umrah a Najeriya, inda kamfanonin jiragen sama suka soke tafiye-tafiyensu zuwa Saudiyya da kasashen Gulf saboda yanayin tsaro.

Mahajjata.
Wasu daga cikin mahajjatan Najeriya yayin da suke shiga jirgin sama Hoto: @NAHCON
Source: Facebook

3. Matsin tattalin arziki da tsadar tafiya

Wani tasiri da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya kan haifar shi ne matsin tattalin arziki, wanda ke jawo tsadar kudin sufuri a kusan duka sassan duniya.

Yakin da ke gudana yanzu haka tsakanin Iran da Isra'ila/Amurka ya haifar da tashin farashin danyen mai a zuwa, kuma hakan na iya kara tsadar kudin sufurin jiragen sama.

Karuwar farashin mai yawanci na haifar da karin kudin tikitin jirgi, wanda zai iya sa yin Umrah ko Hajj ya kara tsada, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Idan kamfanonin jiragen sama sun tilasta canza hanyoyin tafiya saboda barazanar tsaro a wasu sararin samaniya, hakan zai kara tsawon tafiya da kuma kudin tikiti.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

Halin da ake ciki a shirin Hajjin 2026

A jadawalin da ta fitar, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudi Arabia (GACA), ta tsara cewa jiragen da ke dauke da maniyyata za su fara isa kasar domin aikin Hajjin 2026 daga ranar 18 ga Afrilu zuwa 21 ga Mayu, 2026.

Da yake magana kan damuwar da wasu ke nunawa dangane da tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya kan aikin Hajjin bana, kwamishinan ayyuka na Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON), Prince Anofi Olabrewaju Elegushi, ya ce ya yi a yanke hukunci tun yanzu.

A rahoton da Tribune Nigeria ta kawo, Elegushi ya ce:

“Ina ganin har yanzu lokaci bai yi ba a yanke shawara game da Hajjin 2026.”

Wasu masu ruwa da tsaki da suka yi magana kan batun sun bayyana fatan cewa rikicin Gabas ta Tsakiya zai kare kafin lokacin Hajjin bana.

Shugaban NAHCON.
Shugaban hukumar alhazan Najeriya, Ambasada Isma'il Yusuf Abba Hoto: @nigeriahajjcom
Source: Twitter

Saudiyya ta soki hare-haren Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Saudiyya ta bayyana cewa Iran za ta fi kowa asara mai girma idan har hare-haren da ake kai wa kasashen yankin Gulf suka ci gaba.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Saudiyya ta yi Allah-wadai da hare-haren da ta kira na rashin tausayi da ake zargin Iran da kai wa Saudiyya da wasu kasashen Larabawa da Musulmi.

Haka zalika, ta bayyana cewa hare-haren da aka kai kan muhimman wuraren jama’a sun saba wa dokokin kasa da kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262