Isra’ila Ta Gano Wani Sabon Salon Yaki da Iran Ke Yi, Ta Fadi Illar da Ta Mata

Isra’ila Ta Gano Wani Sabon Salon Yaki da Iran Ke Yi, Ta Fadi Illar da Ta Mata

  • Isra’ila ta zargi Iran da kutsawa cikin kyamarorin tsaro da dama domin leƙen asiri tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya
  • Kamfanin tsaron yanar gizo na ya ce masu kutse sun yi amfani da kyamarori domin tattara bayanai kan wuraren hari
  • Rahoto ya ce Isra’ila ma ta taba yin kutse a kyamarorin zirga-zirga a Tehran kafin harin da ya kashe Ali Khamenei

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Isra'ila - Hukumar kula da tsaron yanar gizo ta Isra’ila ta ce ta gano hare-haren kutse da dama daga kasar Iran.

Hukumar ta ce ana kutse a cikin kyamarorin tsaro domin leƙen asiri tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta zargi Iran da yi mata kutse
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

A wani sako da aka wallafa a shafin X, kungiyar Cyber Israel ta ce tana sanar da daruruwan masu kyamara domin su canza lambobin sirrinsu tare da sabunta manhajojin su domin kauce wa hadarin tsaro.

Kara karanta wannan

Iran ta yi martani ga barazanar Trump, ta magantu kan kawar da shi a doron kasa

An gano kutsen da Iran ke yi wa Isra'ila

Hukumar ta bayyana cewa an gano dozin-dozin na kutsen Iran cikin kyamarorin tsaro, lamarin da ya sa ta bukaci jama’a su kasance cikin shiri.

Ta ce hakan na da muhimmanci domin kare tsaron kasa da kuma na mutane da kansu.

Hare-haren yanar gizo tsakanin Iran da Isra’ila sun zama ruwan dare a cikin ‘yan shekarun nan, yayin da kasashen biyu ke gudanar da wani irin yakin boye da boye.

Wannan rikici ya kai ga barkewar yaki a bayyane a watan Yuni na bara, sannan kuma ya sake tsananta a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Masana sun ce masu kutse da ke da alaka da Iran sun kara kaimi wajen kai hare-haren yanar gizo a yankin tun bayan da aka fara hare-hare kan Iran.

Isra'ila ta gano salon yaki da Iran ke yi mata
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da na'urar CCTV. Hoto: @netanyahu, @Israel_Cyber.
Source: Twitter

Yadda Iran ke yi wa Isra'ila kutse

Kamfanin tsaron yanar gizo na Isra’ila ya ce tun bayan fara hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, an ga masu kutse suna shiga cikin kyamarorin sa ido.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Rahoton ya ce ana yawan amfani da irin wadannan kyamarori amma sau da yawa ba a tsare su da kyau ba.

Shugaban sashen leƙen asirin yanar gizo a kamfanin, Gil Messing, ya ce ana iya amfani da hotunan da aka samu daga kyamarorin domin tantance irin barnar da hare-hare suka yi.

Haka kuma ana iya amfani da su domin tattara bayanai kan halayen mutane ko wuraren da za a kai hari.

Messing ya kara da cewa yawancin wadannan masu kutse suna da alaka da rundunar sojin Iran kuma suna samun goyon bayan gwamnati.

Iran ta gano dalilin kai mata hari

Kun ji cewa yankin Gabas ta Tsakiya ya tsinci kansa cikin rikici sakamakon yakin da Amurka da Iran suka kaddamar a kan kasar Iran.

Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya bayyana manufar da Amurka da Isra'ila ke son cimmawa sakamakon kai hare-haren.

Gholamreza Mahadavi Raja ya bayyana cewa hare-haren na Amurka da Isra'ila na shafar fararen hula a kasar Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.