Abin da Putin Ya Tattauna da Shugaban Iran yayin da Ake Yaƙi da Isra'ila

Abin da Putin Ya Tattauna da Shugaban Iran yayin da Ake Yaƙi da Isra'ila

  • Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya kira waya inda suka tattauna da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian kan yakin da ake yi
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa Putin ta tattauna da Pezeshkian kan yakin Iran da Isra'ila mai goyon bayan kasar Amurka
  • Fadar Kremlin ta ce yayin tattaunawar, Putin ya jaddada matsayinsa na goyon bayan dakatar da rikicin da wuri domin rage tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi wata muhimmiyar tattaunawa ta waya da shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

An tabbatar da cewa Putin ya tattauna da Shugaba Masoud Pezeshkian kan batun yakin Iran da Isra'ila wanda ya jawo martani daga ko ina a fadin duniya.

Putin ya kira Shugaban Iran a waya kan yaki da Isra'ila
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha. Hoto: Anadolu Agency.
Source: Facebook

Tattaunawar Putin ta waya da shugaban Iran

Rahoton Al Jazzera ya ce fadar Kremlin ta bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da ake ciki na rikice-rikicen yankin da bukatar dakile tashin hankali.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sojojin Iran sun ja kunnen Trump kan neman tsayar da yaki

A cewar Kremlin, Putin ya sake jaddada matsayinsa na cewa ya kamata a dakatar da rikicin cikin gaggawa domin hana kara tabarbarewar tsaro.

Shugaban na Rasha ya kuma bayyana cewa mafita mafi dacewa ita ce warware rikicin ta hanyar siyasa, tattaunawa da diplomasiyya maimakon amfani da karfin soji.

Putin ya kira shugaban Iran a waya
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a gidan gwamnati Hoto: Gavril Grigoroc.
Source: Getty Images

Yakin Iran/Isra'ila: Tabbacin da Putin ya bayar

Putin ya kara da cewa Rasha na ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri da zai kai ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Sanarwar ta ce:

“Shugaban ƙasar Rasha ya sake jaddada matsayinsa na ƙa’ida cewa dole ne a gaggauta rage zafin rikicin, kuma a warware shi ta hanyoyin siyasa.
Masoud Pezeshkian ya gode wa Rasha bisa goyon bayan da take bai wa Iran, musamman wajen tura taimakon jin kai zuwa ƙasar.”

Wannan kiran waya tsakanin shugabannin kasashen biyu shi ne na biyu tun farkon wannan watan, bayan wani tattaunawa da suka yi, cewar rahoton Asia Pacific.

Rikicin yankin ya kara tsananta bayan Isra’ila da Amurka sun kaddamar da harin hadin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, inda aka kashe sama da mutane 1,200 zuwa yanzu, ciki har da Ali Khamenei wanda shi ne jagoran addinin Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta yi zargin an yi karya da sunanta a harin da aka kai Turkiyya

Duk da haka, Tehran ta ki mika wuya, inda ta mayar da martani da hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami kan Isra’ila da kuma kasashen Gulf da ke dauke da sansanonin sojin Amurka, lamarin da ya dagula kasuwannin duniya.

Amfanin da Rasha ke samu a yakin Iran/Isra'ila

A wani labarin, ana ganin kasar Rasha ce a sahun farko wajen cin gajiyar yakin da ke kara tsananta tsakanin Amurka/Isra'i'la da kasar Iran.

Shugaban Majalisar tarayyar Turai, Antonio Costa ya ce Rasha tana amfana da wannan yaki ta bangarori daban-daban duk asarar da ake tafka wa.

A cewar Costa, farashin mai da ya karu ya samar wa Rasha karin kudaden shiga, sannan kuma Amurka ta dakatar da taimakon Ukraine.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.